Isaac Fayose ya caccaki ɗan uwansa Ayo Fayose kan kalaman da ya yi game da sace ɗalibai a Oyo

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Dan kasuwa kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Isaac Fayose, ya soki ɗan’uwansa kuma tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, kan kalaman da ya yi dangane da sace ɗalibai da malamansu a Jihar Oyo.

A wata hira da ya yi a gidan talabijin ranar Talata, Ayo Fayose ya yi zargin cewa sace ɗalibai 46 da malamansu a Oyo na iya kasancewa wani shiri ne da gwamnatin jihar ta ƙulla domin kunyata Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Tsohon gwamnan ya kuma yi tambaya kan yadda gwamnatocin jihohi ke amfani da kuɗaɗen tsaro da suke samu wajen magance matsalar rashin tsaro a yankunansu.

Sai dai cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta bayan hirar, Isaac Fayose ya nuna rashin jin daɗinsa da kalaman ɗan’uwansa, yana tambayar dalilin yin irin waɗannan zarge-zarge ba tare da hujja ba.

Ya ce idan za a riƙa ɗaukar irin wannan zato, to ya kamata a yi irin waɗannan tambayoyin game da sace-sacen mutane da suka faru a jihohin da jam’iyyar APC ke mulki, ciki har da Kwara, Neja da Borno.

Isaac Fayose ya bayyana cewa kalaman ɗan’uwansa ba su da amfani, yana mai ba shi shawarar ya guji yin maganganu kan batutuwan da ba shi da tabbatacciyar hujja a kansu.

A cewarsa, tsofaffin gwamnoni da ba su da wani muhimmin abin da za su ƙara a tattaunawa kan muhimman batutuwan ƙasa ya kamata su yi shiru maimakon yin maganganun da za su iya tayar da ƙura.

Bidiyon ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke goyon bayan Isaac Fayose yayin da wasu kuma ke kare Ayo Fayose.

Isaac Fayose ya wallafa bidiyon tare da rubuta cewa: “My brother shame dey shame me. Abeg hear my brother.”

Masu amfani da kafafen sada zumunta da dama sun yi tsokaci kan lamarin, inda wasu suka yaba wa Isaac Fayose saboda abin da suka kira tsayawa kan gaskiya ko da kuwa ya shafi ɗan uwansa, yayin da wasu suka soki Ayo Fayose kan yadda ya yi siyasantar da batun satar ɗaliban.

Lamarin ya sake tayar da muhawara kan matsalar rashin tsaro da kuma yadda shugabanni da masu ruwa da tsaki ke mayar da martani ga irin waɗannan abubuwa masu matuƙar muhimmanci ga rayuwar al’umma.

By ukarofi