
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Alhamis aka samu hatsaniya a Majalisar Wakilai bisa zargin wasu mambobi da karɓar cin hancin Dala 50,000 domin zaɓar Ikenga Ugochinyere a matsayin sabon jagoran marasa rinjaye.
An zaɓi Ugochinyere ne a matsayin jagoran bayan ‘yan majalisa 61 cikin 80 sun nuna goyon bayansu a gare shi da jam’iyyun da ba su yi shura ba sosai bayan Kingsley Chinda ya yi murabus, kamar yadda aka sanar a ranar Talata.
Saidai an samu hayaniya a zauren majalisar a lokacin da Philip Agbese ya nemi a cire sunansa daga cikin waɗanda suka amince wa Ugochinyere bayan an yi zargin karɓar cin hancin.
Ya bayyana zargin a matsayin babban al’amari da ya dace a gudanar da bincike a kai domin kare mutuncin majalisar, kalmomin da wasu tsirarun ‘ya’yan gidan suka goyi baya tare da kira da a miƙa batun ga kwamitin ladabtarwar majalisar.
To saidai a nasa ɓangaren, Ugochinyere ya nuna ƙin amincewa shawarar, lamarin da ya tayar da ƙura a zauren inda wasu suak bayar da shawarar a ba Ugochinyere damar sauraro ba’asinsa akan batun.
