Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar Manoma ta ƙasa ta Nijeriya (AFAN) ta yi gargaɗin cewa samar da abinci a Nijeriya a kakar noma ta 2026 na fuskantar babbar barazana sakamakon tsadar kayan noma, matsalolin tsaro, sauyin yanayi da kuma ƙarancin damar samun kuɗaɗen tallafin noma.
Kungiyar ta bayyana cewa haɗuwar matsin tattalin arziki da matsalolin tsaro na iya kawo cikas ga ƙoƙarin ƙara yawan amfanin gona da kuma tabbatar da wadatar abinci a faɗin ƙasar.
Mataimakin Shugaban ƙungiyar Manoma ta ƙasa (AFAN), Daniel Okafor, ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai kan ƙalubalen da manoma ke fuskanta yayin da ake fara kakar shuka.
Ya ce, tsadar kayan noma, musamman taki, ingantattun iri da magungunan kariya daga kwari da cututtuka, na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar manoma a bana.
A cewarsa, kuɗin ɗaukar ma’aikatan gona ma ya yi tashin gwauron zabi, lamarin da ke ƙara wa ƙananan manoma nauyin kashe kuɗi wajen noma. Ya bayyana cewa irin waɗannan manoma ne ke samar da sama da kashi 70 cikin 100 na abincin da ake ci a Nijeriya.
Wannan gargaɗi na zuwa ne yayin da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa ke ci gaba da nuna damuwa kan yiwuwar ƙaruwar matsalar yunwa a Nijeriya.
Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar ɗinkin Duniya (FAO) tare da abokan hulɗarta sun yi hasashen cewa kimanin mutane miliyan 35 a Nijeriya na iya fuskantar matsananciyar yunwa tsakanin watan Yuni da Agustan 2026 idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba.
Okafor ya ce, sauye-sauyen da ake samu a kasuwannin taki na duniya har yanzu na ci gaba da tasiri wajen hauhawar farashinsa a cikin gida.
Tun da farko, ƙungiyar Raya Juyin Juya Halin Noma a Afirka (AGRA) ta yi gargaɗin cewa rikice-rikicen siyasa da yaƙe-yaƙe a Gabas ta Tsakiya na iya kawo cikas ga samar da taki a duniya, wanda hakan zai janyo ƙarin tashin farashi a ƙasashe masu tasowa ciki har da Nijeriya.
“Tsadar kayan noma, kuɗin aiki da kuma matsalolin sauyin yanayi za su kasance manyan ƙalubale a bana. Batun samun kuɗaɗen tallafi ma kullum matsala ce domin yawancin manoma ba sa samun damar karɓar rance ko tallafin kuɗi,” inji shi.
Ya kuma jaddada cewa rashin tsaro na ci gaba da zama babban ƙalubale ga manoma a yankuna da dama na ƙasar nan.
A cewarsa, yawaitar garkuwa da mutane, hare-haren ’yan bindiga da kuma kai farmaki kan al’ummomin karkara ya tilasta wa manoma da dama barin gonakinsu ko rage yawan filayen da suke nomawa.
Okafor ya ce, tsoron hare-hare ya sa manoma da yawa ba sa iya shiga gonakinsu yadda ya kamata a wannan kakar shuka.
“Rashin tsaro ya kai matsayin da manomi idan ya fita gona ba ya da tabbacin zai dawo gida lafiya ko kuma ba za a sace shi domin neman kuɗin fansa ba,” inji shi.
Haka kuma ya nuna damuwa kan jinkirin fara samun ruwan sama a wasu yankunan ƙasar, yana mai danganta hakan da sauyin yanayi da kuma canje-canjen yanayin damina.
Ya ce duk da cewa watan Mayu ne galibi ake fara gudanar da ayyukan noma sosai a sassa da dama na Nijeriya, har yanzu ba a samu daidaitaccen ruwan sama a wasu yankunan noma ba.
Masu ruwa da tsaki a fannin noma sun ci gaba da kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen samar da tsaro a yankunan karkara, ta faɗaɗa damar samun rance mai sauƙi da kayan noma masu rahusa ga manoma, tare da zuba jari a hanyoyin noma masu dacewa da sauyin yanayi domin kauce wa ƙara tsanantar matsalar ƙarancin abinci a shekara mai zuwa.
