Amurka ta soke tikitin Kofin Duniya da aka ware wa Iran kwanaki kaɗan gabanin gasar

Spread the love

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta kasar Iran ta ce ƙasar Amurka ta soke kaso mai yawa na tikitin da aka ware wa magoya bayanta, domin kallon wasannin rukuni na gasar Kofin Duniya, tana mai zargin ɗaya daga cikin ƙasashen da ke karɓar baƙuncin gasar Amurka da hana magoya bayan nata damar halartar wasannin.

Ana ganin hakan a matsayin matakin da aka ɗauka saboda tsamin dangantakar difulomasiyya da ke tsakanin ƙasashen biyu.

A cewar hukumar, Amurka ta sanya wasu matsalolin gudanarwa da na takardu da suka shafi shiga ƙasar ga tawagar Iran a babbar gasar ta Duniya, ciki har da ƙin ba wa wasu daga cikin ma’aikatan tallafi na tawagar bizar shiga ƙasar.

Wannan na zuwa ne yayin da rikicin tsakanin Amurka da Isra’ila da kuma Iran a gefe guda ke cigaba gudana, wanda aka fara tun ƙarshen watan Fabrairu.

Hukumar Ƙwallon Kafa ta Iran ta kuma bayyana cewa, dokokin Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) sun tanadi a ware wa kowace ƙasa mai halartar gasar kaso takwas bisa 100 na tikitin kowane wasa domin ta rarraba su ga magoya bayanta.

By Babaji

Leave a Reply