Jagoran ‘yan bindiga, Kachalla ya bada sharuɗɗan sako Janar Rabe da iyalinsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanannen jagoran ‘yan bindiga a Jihar Katsina, Muhammad Kachalla ya bayar da sharaɗi na musamman akan sako Manjo-Janar Abubakar Rabe (mai ritaya) da matarsa, Hajiya Amina Abubakar.

A cewar Kachalla, ya tattauna da iyalan mutanen biyu bayan garkuwa da su.

Manjo-Janar Rabe, wanda shi ne tsohon Daraktan hulɗa da jama’a na hedikwatar tsaro, an sace shi ne da iyalin nasa da kuma direbansa, Abdullahi Sa’idu a lokacin da suke kan hanyar koma wa Katsina daga Kaduna, lokacin da ‘yan bindigar suka yi wa motarsu ƙawanya a yankin Kafin-Soli da ke Ƙaramar Hukumar Matazu a Jihar Katsina.

An farmaki tsohon sojan ne a kusa da ƙauyen Zakin Ɓaure, inda ‘yan bindigar suka yi kwanton-ɓauna suka tare hanyar tare da buɗe wuta wa motar, lamarin da ya tilasta mata tsayawa da kuma tsira da direban nasa ya yi da raunin harbin bindiga.

A ranar Asabar ne iyalai da makusantan suka shiga damuwa bayan ‘yan bindigar sun bayyana bidiyon minti huɗu da ke nuna Janar Rabe da matar tasa a komarsu.

Kachalla, wanda shi ma ɗan Matazu ne, ya nemi da a gaggauta sako masa dabbobinsa da ya ce an karɓe yayin atisayen jami’an tsaro a kasuwar ƙauyen Jiƙamshi a kwanan nan.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin Katsina da jagororin ƙananan hukumomin Matazu, Musawa, Charanchi, da Kankia da su tabbatar da biyan buƙatar da ya gabatar domin sako mutanen.

Haka kuma, Janar Rabe a faifan, ya faɗa wa gwamnatin cewa a ‘yan bindigar a shirye suke su amsa wa tattauna ta sulhu domin samun zaman lafiyar al’umma.

By Babaji

Leave a Reply