Shugaban NUJ a Nasarawa ya yaba wa Sunday John kan yaƙin neman zaɓe mai ma’ana

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Lafia

Shugaban ƙungiyar ‘yan jarida(NUJ) reshen Jihar Nasarawa Comrade Salihu Alƙali ya yaba wa tawagar ɗan takar shugaban ƙungiyar Sunday John bisa gudanar da yaƙin neman zaɓe dake mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi jin daɗin ‘yan ƙungiyar a jihar baki ɗaya.

Alƙali ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Lafia babban birnin Jihar yayin da tawagar “Team Sunday John for NUJ Chairman” a turance ta kai ziyarar yaƙin neman zaɓe zuwa gidan rediyon Precious FM Chapel.

Ya kuma shawarci sauran ‘yan takara masu neman muƙamai daban-daban a NUJ da su bi wannan hanya ta yaƙin neman zaɓe da ya dogara kan batutuwa masu ma’ana domin kada a haifar da saɓani a tsakanin ‘yan ƙungiyar.

Shugaban NUJ ɗin ya kuma buƙaci ɗan takarar ya tabbatar ya cika duka alƙawurransa sannan ya bai wa jin daɗi da walwalar ‘yan ƙungiyar fifiko idan ya lashe zaɓen dake tafe.

Alƙali ya jaddada cewa nasarorin da aka samu a cikin shekaru shida da suka gabata na mulkinsa nasara ce ta haɗin gwiwa da aka samu tare da goyon bayan shugabannin zartarwa irin su shi Sunday John.

Ya kuma faɗi cewa ya kamata a tabbatar da sauyin mulki cikin lumana kafin zaɓen ranar 20 ga Yuli, sannan ya buƙaci dukkan ‘yan takara da su bai wa haɗin kan ƙungiyar fifiko.

Shugaban ya yi amfani da wannan dama wajen shawartar ‘yan takaran shugabancin da su haɗa kai su guji yaƙin neman zaɓe mai tsanani da zai raba ‘yan kungiyar.

Yace zaɓen da ke tafe ya kamata ya zama fili na ƙarfafa zumunci a tsakanin ‘yan NUJ ba wajen haifar da rashin jituwa ba.

A nasa ɓangaren, ɗan takar shugaban NUJ a jihar ta Nasarawa Sunday John ya gabatar da tsarinsa na “cigaba da sabbin ra’ayoyi” da nufin bunƙasa gine-gine da inganta walwalar ‘yan ƙungiyar domin inganta yanayin aiki ga dukkan ‘yan jarida a jihar.

Ya yi alƙawarin kare mutuncin ƙungiyar sannan ya tabbatar wa ‘yan ƙungiyar cewa idan aka zaɓe shi zai yi aiki wajen kai ƙungiyar zuwa mataki mafi girma a jihar.

John wanda ma’aikaci ne a hukumar labaran Nijeriya (NAN) kuma shine sakataren NUJ na yanzu a jihar yana yaƙin neman zaɓe karkashin tutar ƙwarewarsa ta shekaru da dama a harkar ƙungiyar wajen bayar da hidima.

Ya bayyana kansa a matsayin shugaban ƙungiya da ya ƙware sosai kuma ginshiƙin goyon baya mai dogaro wanda ya sanya kansa a matsayin wanda yafi dacewa ya gaji shugabancin dake barin mulki.

Ya ce ya shirye ya karɓi ragamar shugabanci bayan yayi aiki cikin nasara a matsayin sakataren ƙungiyar ta ‘yan jarida a jihar a cikin shekaru shida da suka gabata.

By ukarofi

Leave a Reply