Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina
Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta kama wasu mutane huɗu da ake zargi da yan ƙungiyar masu satar motoci da kuma dillancin miyagun ƙwayoyi a yankin Funtua.
A cewar sanarwar da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar a ranar jami’an ofishin ’yan sanda na Central Police Station da ke Funtua sun kama wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi mai suna Aliyu Umar, wanda aka fi sani da “Makami”, bayan samun sahihan bayanai kan ayyukansa a yankin Jabiri da ke hanyar Funtua zuwa Sokoto.
Binciken da yan sanda suka gudanar ya kai ga kwato ƙwayoyin Exol guda 38, ƙunshi 28 na busassun ganyen da ake zargin tabar wiwi ne da kuma wuka mai kaifi. ‘Yan sanda na zargin mutumin na daga cikin manyan masu safarar miyagun ƙwayoyi a yankin, yayin da ake ci gaba da bincike.
A wani samame na daban, jami’an ’yan sanda na Makera Division sun kama mutane uku da suka haɗa da Salim Umar wanda aka fi sani da “Dan Salim”, Yusuf Mustapha mai lakabin “Tatto” da kuma Gaddafi Idris wanda aka fi sani da “One Love”, bayan samun rahoton ɓullar wasu da ake nema ruwa a jallo kan laifukan ƙwacen wayoyi, satar babura, fasa shaguna da kuma fashi da makami.
Kayan da aka kwato daga hannunsu sun haɗa da manyan wuƙake guda biyu, adduna uku, almakashi biyu, sandar karfe, fitilu guda biyu, wayoyin android guda uku, wayoyin maɓalli guda uku, power bank, agogon hannu, cajar kwamfuta, katinan ATM na Opay guda biyu, layukan waya 44, laya da kuma kuɗi har Naira 36,870.
Bincike ya kuma nuna cewa ana zargin su da fasa wani shago da ke kan titin Bishir Idris a Funtua tare da sace kaya da kudi, da kuma ƙwace wani babur ƙirar Boxer mai darajar Naira miliyan 1.1.
Rundunar ta bayyana cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike. Kwamishinan ’yan sanda, CP Ali Umar Fage, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da ayyukan saboda ƙwarewa da gaggawar ɗaukar mataki, tare da jaddada ƙudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar Katsina.
Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin yaƙi da masu aikata laifuka a faɗin jihar katsina.
