Sanannen Malamin addini, Sheikh Maibarga ya rasu a hannun ‘yan bindiga

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shahararren malamin addinin Musulunci kuma mamban ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Ikamatis-Sunnah (JIBWIS), Sheikh Muhammad Maibarga ya rasu a komar ‘yan bindiga bayan garkuwa da shi a Jihar Kebbi.

Rahotanni sun bayyana cewa, an sace malamin tare da abokinsa, wanda tsohon Shugaban jam’iyyar APC ne na Koko/Besse na jihar, lamarin da ya haddasa damuwa acikin mazauna da sauran al’ummar Musulmi.

An tabbatar da rasuwarsa ne a yau Laraba yayin da danginsa da abokan arziƙi ke ƙoƙarin ceto shi daga hannun ‘yan garkuwar.

A wani bidiyo da ‘yan bindigar suka fitar gabanin rasuwarsa, an ga yadda malamin yake fama da matsanancin rashin lafiya, lamarin da ya haifar da tsoro yayin da ake tattauna batun sako shi.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, Kakakin Rundunar ‘Yan sandan Kebbi, SP Bashir Usman ya ce hukumomi na sane da rahotannin da suka shafi tsananin rashin lafiyar malamin da kuma mutuwarsa a hannun ‘yan bindiga.

Wani abokin marigayin mai suna Usman Aliyu, ya ce makusantan marigayin suna ƙoƙarin cika sharuɗɗan ‘yan bindigar na sako malamin ne a lokacin da suka samu labarin rasuwarsa.

A cewarsa, an cigaba da tattaunawar sako malamin kuma dangin nasa suna ƙoƙarin harhaɗa kuɗaɗen da aka buƙata daga ‘yan bindigar.

Wannan al’amari ya jefa makusantan nasa da sauran al’umma cikin jimamin rashin shehin wanda ake girmamawa, lamarin da ya ƙara nuna yadda al’amarin taɓarɓarewar tsaro ya yi ƙamari a sassan shiyyar Arewa maso Yamma, inda garkuwa da mutane da neman biyan kuɗin fansa suka zama ruwan dare.

By Babaji

Leave a Reply