Nijeriya na nazarin maida martani kan cin zarafin ’yan ƙasarta a Afirka ta Kudu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana matuƙar damuwarta kan ci gaba da hare-hare, cin zarafi da tsoratar da ’yan Nijeriya mazauna Afirka ta Kudu ke fuskanta, tana mai bayyana cewa tana nazarin yiwuwar ɗaukar matakan martani kan lamarin.

Ministar Harkokin Waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ce ta bayyana hakan a ranar Litinin yayin da take ganawa da wakilan kafafen yaɗa labarai a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja.

Ta ce duk da cewa gwamnatin na duba yiwuwar ɗaukar matakan ramuwar gayya, duk wata matsaya ta ƙarshe za ta buƙaci tattaunawa da amincewa daga manyan hukumomin gwamnati, ciki har da Majalisar Dokokin Tarayya.

Ministar ta bayyana cewa rashin jin daɗin Nijeriya ya samo asali ne daga irin rawar da ƙasar ta taka a baya wajen taimakawa gwagwarmayar kawo ƙarshen mulkin wariyar launin fata da kuma samun ’yancin kai a Afirka Ta Kudu.

“Nijeriya ta sadaukar da abubuwa masu yawa domin taimakawa Afirka Ta Kudu wajen samun ’yanci. Mun kashe kuɗaɗe da albarkatu masu yawa, har ma mun ware guraben karatu ga ɗaliban Afirka Ta Kudu. A zamaninmu, muna gudanar da zanga-zanga da gangami domin nuna goyon baya ga gwagwarmayarsu,” inji ta.

Ta ƙara da cewa, abin takaici ne yadda ake ci gaba da nuna wariya ga baƙar fata ’yan ƙasashen waje, musamman ’yan Nijeriya, maimakon sauran baƙin hauren da ke zaune a ƙasar.

Da aka tambaye ta ko Nijeriya na tunanin ƙaƙaba takunkumi ga Afirka Ta Kudu, Odumegwu-Ojukwu ta ce har yanzu ana nazarin batun.

“Wannan batu na kan tebur. Sai dai duk wata matsaya za ta fito ne daga matakin koli na gwamnati tare da sa hannun Majalisar Dokoki,” ta bayyana.

Ministar ta kuma bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta kafa sashen kula da rikici a Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Johannesburg da kuma Jakadancin Nijeriya da ke Pretoria bayan ƙaruwar rahotannin hare-hare da cin zarafin ’yan Nijeriya.

A cewarta, ana ci gaba da tattara bayanan ’yan Najeriya da abin ya shafa a sassa daban-daban na Afirka Ta Kudu tare da taimaka musu wajen samun ayyukan ofisoshin jakadanci da kuma shirye-shiryen dawo da su gida idan suna da buƙatar hakan.

Ta bayyana cewa ana ci gaba da tantance mutanen da za a dawo da su Nijeriya tare da haɗin gwiwar hukumomin shige da fice na Afirka Ta Kudu.

Da take mayar da martani kan ikirarin wasu jami’an Afirka Ta Kudu cewa yawancin ’yan Nijeriya da ke neman dawowa gida ba bisa ƙa’ida suke zaune a ƙasar ba, Ministar ta yi watsi da zargin, tana mai cewa ba gaskiya ba ne.

Ta ce mafi yawan waɗanda abin ya shafa ’yan kasuwa ne da mazauna ƙasar bisa doka, amma sun zama waɗanda ake kai wa hare-hare da cin zarafi.

“’Yan Nijeriya da ke gudanar da halastattun kasuwanci ne ake wawure musu shaguna, ana ƙona kadarorinsu, ana tsoratar da iyalansu. Wasu yara ma ba sa iya zuwa makaranta saboda fargabar tsaro. Don haka ba daidai ba ne a ce su baƙin haure ne marasa takardu,” inji ta.

Odumegwu-Ojukwu ta ƙara da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da kare muradun ’yan Nijeriya a ƙasashen waje, tare da ɗaukar matakan diflomasiyya da na jinƙai domin tabbatar da lafiyarsu da haƙƙoƙinsu.

By ukarofi