
Shugaban Kasuwar Zamani ta Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano, Alhaji Garba Tukur, ya ce sauran ‘yan kasuwa da ba su mallaki shagunansu ba suna gab da mallaka.
Shugaban kasuwar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gana wa da Jami’ar Yaɗa Labaran yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, a bisa ziyarar gani da ido sakamakon ginin shagunan da ake ta yi ka’in da na’in a cikin kasuwar a halin yanzu.
Da yake jawabi, Alhaji Garba Tukur, ya kara da cewa, tsaikon da aka samu wajen mallaka wa sauran ‘yankasuwar shagunansu, ya biyo bayan cigaba da tantance ‘yankasuwar da ake ci gaba da yi, yana mai cewa tun da farko an yi la’akari da rashin wadatattun shaguna a cikin kasuwar bayan an zamanantar da ita tare da fitar da layika da hanyoyin motoci da magudanar ruwa a cikin kasuwar, domin ta zamto cikin tsari da ƙa’ida ne ya haifar da haka.
“An zamantar da kasuwar ne shi ya sa aka samu ƙarancin shaguna sakamakon; hanyoyi da magudanan ruwa da aka fitar domin samar da zaman lafiyar kasuwar ta fuskar tsabta da tsaro. Duka shagunan da aka yi ƙasa da sama na bene a inda aka yi su bai kai kaso ɗaya bisa ukun kasuwar ba, to duk abin da muke magana in Allah ya yarda nan da sati uku (3) in sha Allahu za a zo a tarar da gurin ‘yankasuwa suna ta hada-hada.” Alhaji Garba Tukur
Daga nan kuma ya ba da tabbacin cewa, ba za a ɗauki lokaci mai tsawo ba za a ƙarasa gina adadadin shagunan da suka rage na sauran ‘yan kasuwar, a filin tasha da aka samar wanda yake jikin kasuwar.
“Ɗanmajalisa ma ya yi magana da ɗankwangilar da zai zo ya ci gaba da aiki, saboda haka ba da daɗewa ba za a fara aikin sauran shagunan da suka rage, kuma in Allah ya yarda za a bai wa kowa shagonsa da izinin Allah.” Alhaji Garba Tukur.
Kazalika, Shugaban kasuwar ya bayyana ɗanmajalisar ba iya gina kasuwar ya tsaya ba, yana kokari wajen samar da wasu ayyukan raya ƙasa a yankin, inda a ƙarshe kuma ya yi musu albishir sakamakon wani gagarumin tagomashi dake tafe nan gaba kaɗan ga haƙiƙanin ‘yankasuwar.
“Ban da wannan ma, a yanzu haka ɗanmajalisar ya sa mun tantance ainahin ‘yankasuwar waɗanda zai bai wa tallafin jari nan da kwana talatin (30) in sha Allahu.”
