‘Yan sanda sun kama budurwa da zargin halaka kakarta ‘yar shekara 97 a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

‘Yan sanda sun kama wata budurwa Aisha Muktar Hassan yar shekara 20 da haihuwa bisa zargin halaka kakarta Hajiya ummukhutsum Hassan mai shekara 97 a garin Daura.

Kamar yadda jami’in yaɗa labarai na rundunar yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar,mahaifin yarinyar Muktar Hassan ya Kai rahoton kisan kan ga ofishin yan sanda da ke Sabon Garin Daura.

DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa saɓani ya shiga tsakanin su inda nan take Aisha Muktar ta ɗauki kujerar katako da buga ma tsohuwar a kai.

Ya ce bayan samun rahoton lamarin nan da nan yan sanda suka garzaya wurin da abin ya faru ,sai acewar DSP Sadiq ko da isar su sun tarar da tsohuwar jina jina kuma bata cikin hayyacin ta,nan take yan sanda suka garzaya da ita asibiti.

Sai dai daga baya likitan da ke asibitin ya sanar da mutuwar matan a cewar DSP Sadiq.

Ya bayyana cewa da zarar yan sanda sun kammala bincike za a gurfanar da wadda ake zargi da kisan kai kotu.

By ukarofi

Leave a Reply