Kisan Janar Rabe: Sojoji sun bazama murƙushe ’yan bindigar Katsina

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Dakarun sojojin haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma (JTF NW) ƙarƙashin Operation FANSAN YAMMA sun fara wani gagarumin farmaki a Jihar Katsina, inda suka lalata maɓoyar ’yan ta’adda da sansanonin adana kayayyakin aikinsu, a wani ɓangare na ƙoƙarin gano da kuma kamo wazanda ake zargi da sace tare da kashe tsohon Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya).

Aikin sojin, wanda aka sanya wa suna Operation CLEAN SWEEP III, na gudana ne a ƙaramar Hukumar Matazu da wasu al’ummomin da ke makwabtaka da ita, inda ’yan bindiga da sauran ƙungiyoyin masu aikata ta’addanci ke gudanar da hare-harensu.

A cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma ƙarƙashin Operation FANSAN YAMMA, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar ranar Litinin, ya bayyana cewa an ƙaddamar da farmakin ne bayan sace tsohon babban hafsan soja tare da matarsa da wasu da ake zargin ’yan ta’adda da ’yan bindiga ne suka aikata.

Sanarwar ta ce manufar wannan farmaki ita ce gano da murƙushe waɗanda ke da hannu a harin, tarwatsa hanyoyin sadarwa da ayyukan ƙungiyoyin masu laifi, tare da dawo da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa.

Tun bayan fara aikin a ranar 14 ga Yuni, dakarun sun gudanar da sintiri na yaƙi, farmakin da aka gina bisa bayanan sirri, kewaye da bincike, da kuma share maɓoyar miyagu a wuraren da aka gano suna fakewa a yankin da rundunar ke aiki.

Sojojin sun kuma bayyana cewa sun samu nasarori masu yawa a yankin Dutsen Dikkawa da sauran al’ummomin da ke kewaye, inda suka kai hare-hare kan sansanonin ’yan ta’adda a ƙauyukan Adua, Nasarawa da Karaduwa.

A yayin farmakin, jami’an tsaro sun gano tare da lalata wurare da dama da ’yan ta’adda ke amfani da su wajen samun kayan rayuwa da kuma adana kayan aikinsu. Hukumomin soji sun ce wannan mataki ya ƙara raunana ƙarfin ayyukan miyagun ƙungiyoyin da ke yankin.

Rundunar ta kuma bayyana cewa ana gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, rundunonin soji na ƙasa da na ruwa da na sama, da kuma shugabannin al’umma, waɗanda gudummawarsu ke taimakawa wajen inganta tsaro a jihar.

Yayin da take sake jaddada aniyarta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, rundunar ta tabbatar wa al’ummar Matazu da maƙwabtan yankin cewa dakarunta za su ci gaba da hana ’yan ta’adda da ’yan bindiga samun damar gudanar da ayyukansu a yankin.

Har ila yau, rundunar ta buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanan sirri da za su taimaka wajen gano da cafke masu aikata laifuka, tana mai tabbatar da cewa za a kiyaye sirrin duk bayanan da aka bayar.

“Dakarunmu za su ci gaba da matsa wa miyagun laifi lamba har sai an cimma duk manufofin wannan aiki,” inji sanarwar.

Hukumomin soji sun ƙara da cewa za su ci gaba da sanar da jama’a sabbin bayanai yayin da aikin ke ci gaba.

By ukarofi

Leave a Reply