Maƙiyan Tinubu ne ke ƙara rura wutar matsalar tsaro a Nijeriya – Akpabio

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi zargin cewa matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a Nijeriya abu ne da maƙiyan Shugaban ƙasa Bola Tinubu ke ƙara rura shi saboda ba su son ci gaban dimokraɗiyya.

Akpabio ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Asabar a lokacin da ake gabatar da litattafai guda uku da aka rubuta domin karrama tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Abdulsalami Abubakar, kuma a matsayin wani ɓangare na bikin cikarsa shekaru 84 a duniya.

Littafin dai ya haɗa da wanda shi Abdusalami ya rubuta na tarihin rayuwarsa.

Abdusalami, wanda janar ne mai ritaya, ya riƙe shugabancin Nijeriya ne daga watan Yunin 1998 biyo bayan rasuwar marigayi shugaban ƙasa Sani Abacha kuma a wannan shekara ne ya miƙa mulki ga tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo a ranar 29 ga watan Mayun 1999.

Wannan mataki ne ya kawo Nijeriya ga tsarin dimokraɗiyyar da take kai a halin yanzu na tsawon shekaru sama da 20. Kuma tun bayan miƙa mulki, Abdusalami ya ci gaba da zama dattijon ƙasa kuma wakilin wanzar da zaman lafiya da ya haɗa da kasancewa shugaban kwamitin zaman lafiya na ƙasa.

A yayin taron, Akpabio ya yaba wa tsohon shugaban kan ƙarfafa dimokradiyya da nuna ƙarfin guiwar da yake yi kan wannan gwamnati da rundunonin tsaro waɗanda za su kawo ƙarshen matsalar tsaro.

“Tilas ne na faɗa cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, yana fama da maƙiya masu yawa da ba sa son cigaba na abin da ka bari. A yau, da yawansu na ɗaukar nauyin matsalar tsaro a Nijeriya domin shafa wa dimokraɗiyya kashin kaji. Amma zan iya faɗa maka cewa da irin jajircewar dakarunmu maza da mata da ke sanye da kaki, maƙiyan da muke da a yau, ba za ci gaba da wanzuwa ba,” ya faɗa.

Shugaban majalisar dattawan ya kuma nuna ƙarfin guiwarsa a kan gwamnati za ta kawo ƙarshen ta’addanci da talauci a yayin da yake kokawa game da illar shan miyagun ƙwayoyi a cikin al’umma.

“Ka hasaso ƙasar da za a ce yaro zai iya kashe mahaifinsa saboda ya sha Tiramadol da sauran ire-irensu. Na ma rasa ta yaya zan yi bayaninsa. Amma zan iya faɗa maka cewa, duk da irin matsalar tsaron da muke fama da ita a yayin da muke da mutane kamar ku, da irin misalin da kuka bar mana a baya, lallai za mu kawo ƙarshen ta’addanci. Za mu kawo ƙarshen talauci a ƙasar nan. Kuma na Nijeriya za ta karɓi kambun da ya kamace ta a duniya.”

Akpabio ya ƙara da cewa ‘yan majalisu suna cin albarkacin harsashin ginin dimokraɗiyyar da Abdusalami ya gina ne inda ya ba shi tabbacin cewa ba za a manta da irin gudunmowar da ya bayar ba.

Kalamansa na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro a Nijeriya ke daɗa ta’azzara duk da irin tabbacin da shugaba Tinubu ke bayarwa na ci gaban da ake samu. Tun watan Mayun 2023, ana ci gaba da samun hare-haren ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a faɗin ƙasar nan da ya shafi jihohi kamar Benuwai da Filato da Zamfara, Katsina, Sakkwato, Kebbi, Borno da sauran sassan Arewa ta tsakiya.

ƙungiyar Amnesty International ta rawaito cewa daga Mayun 2025 an kashe mutane aƙalla 10,217 a hare-hare daban-daban a cikin shekaru 2 na gwamnatin Tinubu. A yayin da kuma jihohin Benuwai da Filato suka fi yawan mutanen da aka kashe. ƙungiyar ta ce an raba mutane ɗaruruwa da gidajensu da kuma da yawa da suka bar ƙauyukansu.

Garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa na ci gaba da zama babban ƙalubale. A cewar cibiyar SBM Intelligence, an sace mutane 4,722 a faɗin Nijeriya a tsakanin watan Yulin 2024 da Yunin 2025, inda aka biya kuɗin fansa na aƙalla Naira biliyan 2.57. rahoton ya kuma bayyana garkuwa da mutane da zama wata masana’antar samun kuɗin mai soka da ke ƙara rura wutar rashin doka da oda da matsin tattalin arziƙi a yayin da manoma abin ke ci gaba da shafarsu wajen zuwa gonakinsu sakamakon hare-hare marasa iyaka.

By ukarofi

Leave a Reply