Nijeriya ta zama ta biyu cikin manyan ƙasashen da suka gaza kaiwa gasar Kofin Duniya ta 2026

Spread the love

Tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya, wato Super Eagles, ta zama ƙasa ta biyu mafi matsayi a jadawalin ƙasashen duniya da ba su samu tikitin shiga gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026 ba, bisa sabon jadawalin matsayi da Hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya, FIFA, ta fitar.

Nijeriya, wadda ke matsayi na 26 a duniya, ita ce ta biyu bayan ƙasar Denmark mai matsayi na 21, a cikin jerin ƙasashen da ke da matsayi mafi girma amma suka kasa samun gurbin shiga gasar da za a gudanar a ƙasashen Amurka, Meziko da Kanada.

Rashin ganin Super Eagles a babbar gasar ƙwallon ƙafa ta duniya ya ci gaba da jawo cece-kuce a tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafa, musamman ganin cewa Nijeriya na daga cikin ƙasashen Afirka da suka yi fice a wannan wasa tsawon shekaru.

Tsohon kyaftin ɗin tawagar Ingila, John Terry, ya bayyana rashin halartar Nijeriya a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwan mamaki a gasar.

A cewarsa, Nijeriya ƙasa ce mai ɗimbin hazaƙa da ƙwararrun ‘yan wasa, kuma da ya so ya ga tana cikin gasar.

“Nijeriya za ta yi matuƙar rashi a wannan gasar. Da gaske na yi fatan ganin ƙasa mai ƙarfi kamar Nijeriya saboda tana da manyan ‘yan wasa masu ƙwarewa kuma ƙasa ce mai tarihi a harkar ƙwallon ƙafa,” inji Terry.

Super Eagles ta rasa damar zuwa gasar ne bayan rashin nasarar da ta samu a wasannin neman tikitin shiga gasar da aka gudanar ƙarƙashin Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF).

Wannan ya sa Nijeriya ta sake rasa shiga gasar Kofin Duniya karo na biyu a jere, bayan ta kasa samun gurbi a gasar ta 2022 da aka gudanar a ƙatar.

Duk da wannan koma baya, Nijeriya na ci gaba da kasancewa cikin manyan ƙasashen Afirka a jadawalin FIFA. A halin yanzu, ƙasar na biye ne bayan Moroko da Senegal, yayin da Algeria da Masar suka cika jerin manyan biyar na Afirka.

Yayin da sababbin matasan ‘yan wasa ke ci gaba da fitowa, hankula sun fara karkata kan yadda za a sake gina Super Eagles domin shirya ta ga manyan gasa masu zuwa.

Masu ruwa da tsaki na ganin cewa sake fasalin tsarin gudanarwa, samar da daidaito a harkokin jagoranci da kuma inganta wasannin neman tikitin shiga manyan gasa za su taka muhimmiyar rawa wajen dawo da Nijeriya cikin manyan ƙasashen ƙwallon ƙafa na duniya.

By ukarofi

Leave a Reply