‘Yan sandan Katsina sun kama ƙasurgumin dillalin ƙwaya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Rundunar ‘yan sanda sun kama Salisu Jibrin Dan shekara 27 da haihuwa ɗauke da haramtacciyar ƙwaya mai suna Diazepam guda 2000 a Funtua.

Kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar, jami’an da ke aiki a ofishin ‘yan sanda a garin Funtua suka kama wanda ake zargi a kan babur na hawa ɗauke da ƙwayar.

Bincike da ‘yan sanda suka gudanar Salisu wanda ake zargi ya shaida cewa wata mata mai suna Faith Eze ta bashi ya kai wa wani mai suna Gurgu.

Tuni dai ‘yan sanda suka kama matan a cewar DSP Sadiq a yayin da an shiga farautar shi Gurgun.

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar CP Ali Umar Fage ya yaba wa jami’an sa bayan nuna ƙwarewa da jaruntaka wajan kamen da suka yi.

Ya sha alwashin yaƙar irin waɗannan miyagun mutane da sauran ɓata gari a faɗin jihar.

CP Fage ya nemi goyon bayan alummar jihar wajen ba jami’an sa bayanai na sirri inda zai kai su ga maɓoyar waɗannan miyagun mutane.

By ukarofi

Leave a Reply