Kano: Tsofaffin ɗaliban makarantar St. Louis sun nemi a binciki mutuwar ɗaliba, Nihal

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Tsofaffin ɗalibai mata ta Makarantar St. Louis (SLOGA) reshen Abuja, tare da tsofaffin ɗalibai, iyaye da masu ruwa da tsaki na St Louis da ke Kano, ta nemi a gudanar da cikakken bincike akan ainihin abin da ya sabbaba mutuwar ɗaliba Maimuna Salisu Yaro mai shekaru 14, wadda aka fi sani ida Nihal.

A wata sanarwa da SLOGA ta aike wa NewsPointNigeria a yau Asabar, ƙungiyar ta ce ta samu labarin mutuwar ɗaliban cikin alhini bayan ababen da suka faru a makarantar a ranar 13 ga watan Yuni, 2026.

Ƙungiyar ta bayyana ɗalibar a matsayin yarinya daga cikin yara, ‘ya, ‘yar aji, ƙawa kuma ƙarama a makaranta da ke buƙatar tsaro, kulawa da kuma kariya daga dukkan wata nau’i ta cutarwa.

A cewar ƙungiyar, abin alhinin ya taɓa tsofaffin ɗaliban bisa kusancinsu ga makarantar, saboda haka ne ta yi kira ga hukumar gudanarwar makarantar da ta ba hukumomin tsaro haɗin kai yayin da suke gudanar da bincike akan al’amarin.

Haka kuma, SLOGA ta buƙaci St. Louis ta Kano da ta fayyace dukkwani bayani da ya shafi al’amarin, tallafa wa iyalan marigayiyar da kuma taimakawa wajen dawo da yardar al’umma akan ƙoƙarinta na tabbatar da gaskiya da adalci.

Rahotannin da ƙungiyar ta samu sun nuna cewa Maimuna ta yanki jiki ta faɗi ne sannan ta rasu bayan wani horo mai tsanani da ta fuskanta akan halartar sallar jam’i a latti.

An yi zargin cewa, hakan ya sa aka tilasta mata sanya gwiwanta a ƙasa na tsawon sa’o’i a ƙarƙashin rana ba tare da ruwa ba, inda daga bisani aka sanar da rasuwarta yayin da aka garzaya da ita wani asibitin kuɗi.

Yayin da ƙungiyar ta yi kira da a kwantar da hankula, ta kuma yi gargaɗin cewa wajibi ne a tabbatar da adalci akan lokaci kuma kada a yi amfani da hanyoyin shari’a wajen bayar da kariya.

Ga jerin waɗanda suka sanya wa takardar sanarwar hannu kamar yadda NewsPointNigeria ta wallafa:
“Aisha Abdallah Lukat — Class of 1986
Saida Sa’ad — Class of 1989
Khadija Dahiru Mustapha — Class of 1990
Rahmatu Maude — Class of 1988
Ramat Jafar Isa — Class of 1994
Maryam Bala Hassan — Class of 1997
Hassana A. Lukat — Class of 1991
Jamila Ahmad — Class of 1994
Alexandria Amanfo — Class of 2000
Halima Iliya Ibrahim — Class of 1989
Habiba Musa Usman — Class of 2000
Zainab Jalingo — Class of 1999
Nabila Muktar Elyakub — Class of 2010
Rukayya Tofa — Class of 2004
Amina Usman — Class of 1988
Surayyah Adamu — Class of 2001
Aishatu Usman — Class of 1990
Rakiya Ahmed — Class of 1988
Rakiyah Ibrahim Hamisu — Class of 1996
Maryam Bashir Umar — Class of 1985
Rayhanah Tahir Abdullahi — Class of 2014
Ramatu Adam — Class of 2006
Maimuna Abdurrahim — Class of 1997
Gladys Eneh-Ani — Class of 1997
Saadatu Hassan — Class of 1991
Zainab Imam — Class of 1988
Asiya Magaji Abdullahi — Class of 1998
Maimuna Zakari — Class of 1997
Rabi Sani — Class of 1994
Binta Shuaibu — Class of 1996
Zaleeha Zakari — Class of 2004
Aisha Hanga — Class of 2005
Fatima Monguno — Class of 1998
Amina Aminu Dorayi — Class of 1993
Rose Okoruwa — Class of 1995″

By Babaji

Leave a Reply