Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Dakarun Operation Hadin Kai sun kashe wasu mutum biyu da ake zargin ‘yan leƙen asirin ƙungiyar ISWAP ne yayin da suke ƙoƙarin shiga Nijeriya daga Kamaru ta kan iyakar jihar Borno.
TheCable ta rawaito cewa dakarun Bataliya ta 152 da ke Banki, tare da haɗin gwiwar mambobin Civilian Joint Task Force ne suka gudanar da samamen.
Majiyoyin tsaro sun shaida wa jaridar Zagazola Makama cewa an tare mutanen ne a ranar 21 ga watan Yuni bayan sun tsallaka daga ɓangaren Kamaru zuwa cikin Nijeriya.
Bayanan sirri da dakarun suka samu sun nuna cewa mutanen na da alaƙa da ƙungiyar ISWAP, kuma ana zargin sun shiga Nijeriya ne domin tattara bayanai kan yadda sojoji ke gudanar da ayyukansu ko kuma domin samar wa ‘yan ta’adda kayayyakin tallafi.
Majiyoyin sun bayyana cewa an hango mutanen suna tsallake katangar iyaka, lamarin da ya sa dakarun suka shirya kwanton bauna tare da buɗe musu wuta. Dukkaninsu sun mutu a yayin arangamar.
Majiyoyin sun ƙara da cewa dakarun na ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana a faɗin yankin domin hana ‘yan ta’adda zirga-zirga da samun kayan aiki.
Sun kuma bayyana cewa duk da samun ɗan kwanciyar hankali a yankin, hukumomin soji na ci gaba da ɗaukar matakan tsaro saboda barazanar da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya ke ci gaba da haifarwa.
Operation Haɗin Kai na ci gaba da kai hare-haren soji da sintiri a yankin Arewa maso Gabas domin dakile zirga-zirgar ‘yan ta’adda ta kan iyaka da kuma raunana ƙarfinsu na gudanar da hare-hare.
