Fitattun taurarin da suka yi ridda: Mene ne alaƙar dake tsakanin fitattun mutanen da suka bar Musulunci?

Spread the love

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS

A makon da ya gabata, mun kawo sunaye da bayanai na wasu fitattun taurari ‘yan Nijeriya da suka fito daga gidajen Musulunci amma daga baya suka bayyana rungumar addinin Kiristanci. Sunayen da suka fito a rahoton sun haɗa da taurarin TikTok, mawaƙa, jaruman fina-finai da kuma wasu daga cikin mashahuran masu tasiri a kafafen sada zumunci. Kowane daga cikinsu ya bayar da nasa dalilin na barin addinin Musulunci, lamarin da ya haifar da ce-ce-kuce a tsakanin mabiya da masoyansu na daga addinan biyu.

Saidai bayan hanayniyar ra’ayoyi da kuma martani, akwai tambayar da ta ke rayuwa zuwa yanzu kawowa yau, wato mene ne ya haɗa waɗanan mutane masu yin ridda wanda ba kasafai ake samun haka ba. Shin kaɗuwar shahara ce kawai ta haɗa su wuri ɗaya? Ko akwai wani abu mai zurfi da yake haɗa labarinsu fiye da yadda ake gani a zahiri?

Da farko mai karatu zai yi tunanin babu wata alaƙa da za ta iya haɗa waɗannan mutane, duba da cewa, akwai tazara mai nisa tsakanin rayuwar Peller da ta Adewale Ayuba. Haka kuma akwai bambanci tsakanin Korae Bello, Tobi Bakre da Sola Allyson ta fuskar sana’a, shekaru, dangantakar jini, da kuma muhallian da suka yi suna a cikinsu. Wato ɗaya daga cikinsu ya yi suna a TikTok, wani a waƙoƙin Fuji, wani ya yi suna a harkan fina-finai, yayin da wata ta zama ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan waƙoƙin bishara a Najeriya.

Saidai idan aka zufafa bincike da hangen nesa za a iya hango inda alaƙar take, kuma da ita ne kawai za a iya kawar da kwankwanton da yake zukatan mutane. Wato inda suka fito. Kusan dukansu sun fito ne a yankin Yarbawa.

Wannan gaskiyar kawai ta isa ta buɗa ƙofa kan warware wasu kwankwamton da yake zukanatan masu mutane musamman daga cikin musulmnai masu ƙarancin ilimi da suke tambayar ya hakan ta faru, ko suke kwankwanton zamewar Muslunci hanyar gaskiya.

Tambayar anan dai ita ce, shin akwai wani abu a cikin tarihin zamantakewar Yarbawa da zai iya bayyana mana dalilin da ke sa yawan sauye-sauyen addini ya zama ruwan dare a cikin al’ummar Yarbawa? Wannan kuwa ba ina magana kan Musulunci kawai ba, domin sau da yawa ana samun sauyin addini daga Kiristanci zuwa Musulunci cikin sauƙi a ɓangaren saɓanin wasu wurare.

Domin samun wannan amsar wajibi ne mu koma baya cikin tarihi na al’ummar Yarbawa da yadda addini ya kasance abu na biyu da suke kallo ba na farko ba.

A wasu sassan Najeriya addini ne kan gaba wurin bayyana mutum tun daga sunansa zuwa aikinsa. Akwai wuraren da addini ba ya bar gurbin da ba za a kalli dangantaka ba ko zamantakewa, wato idan ba ka bi addini ba to tamkar ka yi sallama da dangantaka da zamantakewa ne. Ma’ana addini ne ke rinjayar dangantakar iyali da ta al’umma. Wannan ne ke sa a duk lokacin da wani ya yi aniyar barin addinisa to fa ya san ya ɗauko dala ba ganwo, al’ummarsa za su yi masa ca har ta kai ya rasa sunansa da gadonsa. Wataƙila wannan ne ke sanya darajar addini tare da riƙo da shi fiye da komai, kasancewarsa sama da al’ada. Hakan ke sa ba kasafai za ka tarar da mace ta yi sha’awar auren wanda ba addininsu ɗaya ba, koda ta yi kuwa tana saurin kawar da zancen duban girman addinin a tsakanin mutanenta.

Saidai ko kaɗan ba haka take ba a cikin al’unmar Yarbawa. Masana tarihi sun bayyana cewa, tun kafin zuwan Turawa da mishanoni, al’ummar Yarbawa sun riga sun yi ginin rayuwarsu mai ƙarfi kan al’ada da dangantaka ta yare, mutunta alaƙar jini da ɗora shi sama da komai. Lokacin da Musulunci ya bazu a yankin, sannan daga baya Kiristanci ya biyo baya, wanzuwar addini bai iya kawar da tsohuwar al’adarsu ba, maimakon haka al’adar ta ci gaba da rayuwa ne tare da addinan biyu, ba tare da bari su zama sama da ita ba.

A duk inda bayarabe yake abu na farko da yake fara dubawa shi ne, kai ɗin bayarabe ne, idan amsar ta zama e, to yana kawar da kansa daga kallon sauran abubuwa, ciki kuwa har da adddini. Wannan ne ya sa tsayin shekaru gidajen Yarbawa suka rayu tsakanin addinai biyu a ƙarƙashin inuwa guda. Akwai gidajen da uwa musulma uba kirista. Wasu kuwa uwar ce musulma uba kirista. A irin wannan yanayi ya ku ke ganin canza addini zai iya zama wani babban abu ga ‘ya’ya?

Akwai wani lokacin da za ka samu duka iyaye musulmai ne, amma sai ɗansu ya waye gari ya yi ridda, wannan kuwa ya fi alaƙa da ababe biyu. Na farko rashin muhinmantar da addinin. Sau da yawa yara a cikin ƙalibar Yarbawa za su taso ba da sanin wani abu sosai game da addini ba, hakan ke kai ga shiga da za ka kasa bambance su da waɗanda ba musulmai ba, a taƙaice dai musulmai ne a baki, amma a aikace ba haka ba ne.

Wannan ne ke sa idan suka shiga cikin mutane sukan zama ɗaya baki ɗaya, inda suke ganin ba abinda ya bambanta su, don haka soyayya za ta iya shiga tsakaninsu ba tare da la’akari da addini ba.

Abu na biyu shi ne cuɗanyar addinan, koda iyayenka duk addini ɗaya suke bi, cikin ‘yan uwanka na kusa nasu ba za a rasa inda addinan biyu suka haɗu ba, don haka za ka yi mu’amala da su ba tare da ƙyama ko ganin rashin dacewar abinda suka yi ba, wannan zai iya kai ka ga aikatawa wata rana.

Za mu ci gaba mako mai zuwa.

By ukarofi

Leave a Reply