
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta amince da aiwatar da manyan sauye-sauye a Hukumar kula da matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), da nufin inganta tsarin gudanar da shirye-shiryenta da kuma daidaita su da buƙatun zamani.
Ministan Ci-gaban Matasa, Mista Ayodele Olawande ne ya bayyana haka ga manema labarai, jim-kaɗan bayan ganawa da Shugaba Bola Tinubu a zaman majalisar zartarwa a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ranar Litinin.
Daga cikin sauye-sauyen da aka amince da su akwai maye gurbin tsarin jagorancin sojoji da na farar hula a hukumar, tare da sake fasalin kayan aikin masu yi wa ƙasa hidima domin su dace da sabon tsarin.
Haka kuma, an bayyana cewa gyaran zai ƙara mayar da hankali kan koyar da sana’o’i, haɓaka ƙwarewar matasa da samar musu da damar dogaro da kai bayan kammala aikin yi wa ƙasa hidima.
Gwamnatin ta ce sauye-sauyen na da manufar ƙarfafa tasirin shirin NYSC wajen bunƙasa matasa, samar da ƙwarewar aiki da kuma ba da gudunmawa ga ci gaban tattalin arziƙi a Nijeriya.
Tun a shekarar 2015 ne aka fara shirin sauya wa hukumar fasali ta yadda za a ga bunƙasa a harkokinta.
