Daga UMAR GARBA a Katsina
Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta kama wata matar aure mai shekaru 23, Sadiya Lawal, bisa zargin yunƙurin kashe mijinta ta hanyar caka masa wuƙa a maqogoronsa yayin da yake barci a birnin Katsina.
Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Abubakar Sadiq, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Litinin.
Sadiq ya ce rundunar ta kama matar auren bisa zargin yunƙurin kisan kai a birnin Katsina.
Mijin mai suna Jamilu Ibrahim, ya kai rahoton matar a sashen ‘yan sanda na babbar kasuwar da misalin ƙarfe 9 na safe a ranar Litinin cewa yana zargin matarsa ta kai masa hari da wuƙa yayin da yake barci a safiyar ranar.
A cewar ‘yan sanda, Ibrahim ya samu babban rauni a wuyansa kuma nan da nan aka garzaya da shi asibiti da ke kusa, inda a halin yanzu yake karɓar magani.
‘Yan sanda sun ce jami’ansu sun ziyarci wurin, sun kama wanda ake zargi, kuma sun gano wuƙar da ake zargin an yi amfani da ita a harin.
Yanzu haka wadda ake zargin na tsare a hannun ‘yan sanda kuma za a gurfanar da ita a gaban kotu bayan an kammala bincike.
DSP Sadiq ya ce, “A yau, 29 ga Yuni, 2026, da misalin ƙarfe 9:00 na safe, wani Jamilu Ibrahim, ya kawo rahoto a sashen ‘yan sanda na babbar kasuwa da ke Katsina, cewa a wannan rana da misalin ƙarfe 5:30 na safe, yayin da yake barci, matarsa, Sadiya Lawal, ‘yar shekara 23, ta kai masa hari da wuƙa inda ta yi ƙoƙarin yanke masa maƙogwaro. Inda ya samu mummunan rauni a wuyansa.
“Bayan samun rahoton, an kai mijin na Sadiya asibiti mafi kusa don ceto ransa inda nan take likitoci suka bashi kulawar gaggawa.
“‘Yan sanda sun ziyarci wurin da abin ya faru, an kama matar da ake zargi, wadda ake zargin ta yi amfani da wuƙa wajen aikata laifin. Yanzu haka ana tsare da ita kuma ana tuhumarta da laifin, inda za a gurfanar da ita a gaban kotu bayan kammala binciken.” In ji kakakin rundunar.
