Sojoji 104 sun ɓace bayan harin Boko Haram a sansanin Borno

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata takardar sirri ta rundunar sojin Nijeriya ta nuna cewa an ayyana sojoji 104 a matsayin waɗanda suka gudu daga bakin aiki bayan wani hari da mayaƙan Boko Haram/ISWAP suka kai sansanin su da ke Jihar Borno.

Rahoton ya ce, sojojin na aiki ne a Bataliya ta 162 ta Rundunar Sojin Ruwa da ƙasa (162 Amphibious Battalion) da ke kan hanyar Mandara–Buratai, inda aka kai harin a ranar 5 ga Yunin 2026.

Bisa ga takardar da SaharaReporters ta ce ta samu, an bayyana cewa sojojin sun bar wuraren aikinsu ba tare da izini ba, tare da makaman da aka ba su, bayan harin da mayaƙan suka kai sansanin. Rahotanni sun ce aƙalla sojoji takwas sun rasa rayukansu a harin.

Wata majiya daga rundunar soji ta bayyana cewa maharan sun kai farmakin ne da misalin ƙarfe 4:00 na asubahin ranar Juma’a, a lokacin da ake ruwan sama. Majiyar ta ƙara da cewa mayaƙan sun kashe sojoji takwas tare da sare musu kawuna, yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban.

Fiye da makonni uku bayan harin, rundunar ta fitar da wata sanarwa mai matakin sirri (Restricted) inda ta ayyana sojojin 104 a matsayin waɗanda suka tsere daga aiki.

A cikin takardar an ce, “Sojan da aka ambata da sauran mutum 103 sun bar wuraren da aka tura su zuwa wani wuri da ba a sani ba a ranar 5 ga Yunin 2026 tare da makaman da aka ba su bayan harin Boko Haram/ISWAP da aka kai sansaninmu.”

Takardar ta ƙara da cewa tun daga wannan lokaci sojojin ba su koma bakin aiki ba, saboda haka aka ayyana su a matsayin masu guduwa daga aikin soja.

Rahotanni sun kuma nuna cewa mahukuntan rundunar sun daskarar da asusun ajiyar kuɗin sojojin da abin ya shafa, tare da umartar dukkan rundunonin da ke sassa daban-daban su cafke duk wani daga cikinsu idan aka gano inda yake. Bayanan da ke cikin rahoton sun nuna cewa cikin sojojin da aka ayyana akwai: Sajan Babba (Staff Sergeant) guda 1, Sajan guda 3, Kofur guda 7, Lance Corporal guda 38, Sojoji masu muƙamin Private guda 55.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Rundunar Sojin Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba. Rahoton ya kuma haɗa da cikakken jerin sunaye da lambobin aikin sojojin 104 da aka ayyana a matsayin waɗanda suka tsere daga aiki bayan harin.

By ukarofi