Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani sabon rahoto mai taken ‘Rahoton Haɗin Kan Al’umma na 2026’ da Cibiyar Binciken Ra’ayin Jama’a ta Afirka (API) ta fitar ya nuna cewa Majalisar Dokoki ta Nijeriya ce hukuma mafi ƙarancin aminci a idon ’yan Nijeriya, inda kashi 77 cikin 100 na masu amsa tambayoyin binciken suka bayyana cewa ba su da cikakken yarda da ita.
Rahoton, wanda aka gabatar a wani taron tattauna haɗin kan al’umma na ƙasa da aka gudanar a Abuja, ya nuna cewa Majalisar Tarayya ta karɓi matsayin da a baya Rundunar ’Yan Sandan Nujeriya ke riƙewa a matsayin hukuma mafi ƙarancin amincewa a tsakanin jama’a.
Babban Daraktan API, Farfesa Bell Ihua, ya bayyana cewa ma’aunin haɗin kan al’umma na Nijeriya (NSCI) ya kai kashi 48.8 cikin 100 a shekarar 2026. Wannan ya nuna ƙarin maki biyu idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata, kuma shi ne mafi girman sakamakon da aka samu tun bayan fara gudanar da binciken.
Sai dai duk da wannan ci gaba, ma’aunin har yanzu bai kai matsakaicin kashi 50 cikin 100 da ake ɗauka a matsayin matakin gamsarwa ba.
A cewar Farfesa Ihua, sakamakon binciken ya nuna cewa har yanzu ’yan Nijeriya na ci gaba da nuna juriya da kuma ƙoƙarin rayuwa tare duk da matsalolin tattalin arziki da zamantakewa da suke fuskanta.
Rahoton ya kuma bayyana cewa jama’a sun fi amincewa da shugabannin addinai da na gargajiya fiye da hukumomin gwamnati. Kashi 51 cikin 100 na mahalarta binciken sun nuna amincewa da shugabannin addinai, yayin da kashi 45 cikin 100 suka nuna amincewa da shugabannin gargajiya.
A gefe guda kuma, kashi 28 cikin 100 ne kawai suka nuna amincewa da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yayin da kashi 23 cikin 100 kacal suka nuna amincewa da Majalisar Tarayya.
An gudanar da binciken ne tsakanin watan Janairu da Fabrairun 2025 tare da tallafin Ford Foundation, inda aka yi hira da mutane 5,315 masu shekaru 15 zuwa sama daga dukkan jihohin Nijeriya ta hanyar ziyartar gidajensu.
Binciken ya gudana ne cikin harsuna biyar da suka haɗa da Turanci, Pidgin, Hausa, Igbo da Yarbanci domin tabbatar da wakilcin al’ummomi daban-daban a faɗin ƙasar.
Dangane da batun asalin ƙasa, rahoton ya nuna cewa kashi 46 cikin 100 na ’yan Nijeriya suna alfahari da ƙasarsu, yayin da kashi 41 cikin 100 suka bayyana rashin jin daɗi game da halin da ƙasar ke ciki. Haka kuma, kashi 44 cikin 100 sun ce suna ganin kansu a matsayin ’yan Nijeriya tare da ƙabilunsu lokaci guda, yayin da kashi 29 cikin 100 suka fi danganta kansu da ƙabilarsu fiye da Nijeriya.
A ɓangaren amincewa da hukumomi kuwa, kashi 72 cikin 100 sun bayyana cewa ba su da cikakkiyar amincewa da gwamnatin Shugaba Tinubu, yayin da kashi 73 cikin 100 suka ce ba su da amincewa da ɓangaren shari’a.
Sai dai duk da waɗannan damuwar, binciken ya nuna cewa akwai alamun ƙarfafa haɗin kai a tsakanin jama’a. Kashi 77 cikin 100 sun bayyana shirinsu na yin aiki tare da mutanen wasu ƙabilu domin gina Nijeriya mai haɗin kai, yayin da kashi 73 cikin 100 suka ce suna shirye su shiga harkokin siyasa domin inganta ƙasar.
Haka kuma, kashi 89 cikin 100 sun nuna goyon baya ga auren tsakanin ƙabilu daban-daban, yayin da kashi 62 cikin 100 suka amince da auren tsakanin mabiya addinai mabambanta.
Rahoton ya kuma nuna cewa bambancin ra’ayin siyasa ne ya fi haddasa rarrabuwar kawuna a cikin al’umma, inda kashi 56 cikin 100 suka bayyana hakan. Bayan haka kuma, bambance-bambancen ƙabila da addini sun biyo baya da kashi 46 da 44 cikin 100 bi da bi.
A ɓangaren daidaito tsakanin maza da mata, kashi 69 cikin 100 sun amince cewa ya kamata mata su samu damar jagoranci a dukkan fannoni na rayuwa, musamman siyasa da harkokin kasuwanci. Haka kuma, kashi 60 cikin 100 sun ce za su iya zaɓar mace a matsayin Shugabar Nijeriya idan ta tsaya takara.
Game da makomar ƙasar kuwa, duk da cewa kashi 45 cikin 100 sun nuna rashin gamsuwa da rayuwarsu a yanzu, rahoton ya nuna cewa kashi 61 cikin 100 suna da yakinin cewa makomar Nijeriya za ta fi yadda take a yau kyau.
Rahoton ya kuma bayyana cewa a karon farko tun bayan fara gudanar da wannan bincike, yawancin mahalarta sun bayyana kansu a matsayin ’yan Nijeriya kafin su ambaci ƙabila, addini ko yankin da suka fito. API ta ce wannan wani muhimmin ci gaba ne a tafiyar gina ƙasa da ƙarfafa haɗin kan al’umma.
A ƙarshe, cibiyar ta ba da shawarar kafa Hukumar Haɗin Kan Al’umma ta ƙasa, wadda za ta mayar da hankali wajen inganta haɗin kai, adalci, amincewa tsakanin jama’a da gwamnati, da kuma tabbatar da cewa manufofin gwamnati sun kasance masu haɗa kowa da kowa.
