Ministan Labarai ya buƙaci masu masana’antar buga takardu su haɗa kai don samun bunƙasa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na ƙasa, Mohammed Idris, ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki a kamfanonin buga takardu ta Nijeriya da su rungumi haɗin kai, sasanci da kuma haɗin gwiwa domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa da kuma ƙara wa fannin ƙarfin gasa a matakin duniya.

Ministan ya bayyana hakan ne a yayin Taron Masu Ruwa da Tsaki na Masana’antar Buga Takardu ta Nijeriya na 2026, mai taken “Daga Sasanci Zuwa Farfaɗowa”, wanda aka gudanar a ranar Talata a Abuja.

Ya ce, warware rikicin shugabanci da ya daɗe yana addabar Cibiyar ƙwararrun Masu Sana’ar Buga Takardu ta Nijeriya (CIPPON) ya samar da wata dama ta musamman da za a sake inganta sana’ar tare da amfani da gagarumar damar tattalin arzikin da ke cikinta.

Ministan ya ce, tarihi ya ba masu ruwa da tsakin wannan dama ta sake fasalin masana’antar, yana mai kira gare su da su yi amfani da ita ta hanyar yin aiki tare da kuma bai wa shugabannin da aka zaɓa cikakken goyon baya domin ciyar da sana’ar gaba.

Mohammed Idris ya tuna cewa ɗaya daga cikin batutuwan farko da aka gabatar masa bayan hawansa kujerar minista shi ne rikicin da ya daɗe yana ci gaba a cikin CIPPON. Ya bayyana cewa, matakin da ya ɗauka na shiga tsakani ya samo asali ne daga imanin cewa tattaunawa da haɗin kai sun fi shari’o’in kotu amfani wajen magance matsalolin da suka dabaibaye masana’antar.

Ministan ya bayyana masana’antar buga takardu a matsayin wani fanni mai matuƙar muhimmanci ga tattalin arziki, wanda kuma ke da damar samar da ayyukan yi ga dubban mutane. Ya ƙara da cewa, idan masu ruwa da tsaki suka kasance da murya ɗaya, hakan zai sauƙaƙa wa gwamnati samar da manufofi da tallafin da za su taimaka wajen bunƙasa masana’antar.

Ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da mara wa CIPPON baya, tare da yin aiki da hukumomin gwamnati da abin ya shafa domin tallafa wa duk wasu tsare-tsare na inganta ƙa’idodin ƙwarewa, kyautata yanayin gudanar da sana’ar da kuma ƙara gudummawar masana’antar ga ci gaban ƙasa.

Haka kuma, Ministan ya buƙaci shugabannin CIPPON da su rungumi salon shugabanci na bai ɗaya, ba tare da nuna bambanci ba, domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa da kuma barin kyakkyawan tarihi da zai amfani ƙarni masu zuwa.

Ya sake jaddada aniyar Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta ƙasa na ci gaba da tallafa wa ƙoƙarin CIPPON na gina masana’antar buga takardu mai ƙarfi, zamani da kuma iya yin gogayya a kasuwannin duniya. Ministan ya kuma shawarci masu sana’ar da su rungumi sabbin fasahohi domin ci gaba da kasancewa cikin sahun gaba a wannan zamani na fasahar zamani.

Tun da farko, Shugaban CIPPON kuma Shugaban Majalisar Gudanarwar cibiyar, Mista Koko T. Clement, ya bayyana cewa tun bayan rantsar da sabuwar Majalisar Gudanarwa a watan Disamban 2025, an samu gagarumin ci gaba.

Ya ce, cibiyar ta yi hulɗa da manyan hukumomin gwamnati domin ƙarfafa ƙa’idojin ƙwarewa, inganta tsarin sa ido kan masana’antar da kuma ingiza manufofin da za su taimaka wajen bunƙasa harkar buga takardu a Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply