ADC ta gudanar da babban taro a Kano, ta soki gwamnatin APC

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta gudanar da wani babban taron siyasa a Kano, inda shugabanni da magoya bayanta suka yi kira ga ‘yan Nijeriya su goyi bayan jam’iyyar a babban zaɓen 2027.

Taron ya samu halartar magoya bayan tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar daga sassa daban-daban na ƙasar.

Da yake jawabi, Alhaji Usman Mado, wanda aka fi sani da Sarkin Yaƙin Atiku, ya ce matsalar tsaro ta ƙara taɓarɓarewa musamman a jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi, Borno da Katsina, inda ya ce hakan ya shafi noma, kasuwanci da sauran harkokin tattalin arziki.

Ya zargi gwamnatin APC da gaza magance matsalolin tsaro da na tattalin arziki, yana mai cewa Nijeriya na buƙatar sabon shugabanci domin ceto ƙasar daga halin da take ciki.

Ita ma Shugabar Mata ta ADC a Kano, Hajiya Aisha Humaira, ta bayyana cewa jam’iyyarsu na da shirye-shiryen samar da tsaro, aikin yi ga matasa da rage tsadar rayuwa idan ta samu damar mulki.

Taron ya samu halartar ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar ADC, Malam Ibrahim Khalil, da wasu ‘yan takarar majalisun dokoki, ciki har da Hon. Rufai, Hon. Rabiu Aminu da Hon. Ibrahim Mustafa, waɗanda suka bayyana cewa sun shiga ADC ne domin samar wa al’umma mafita tare da kawo sauyi a harkokin mulki.

Sun yi kira ga al’ummar Nijeriya da su marawa jam’iyyar baya a zaɓe mai zuwa domin ciyar da ƙasa gaba.

By ukarofi

Leave a Reply