An kama mai ƙosai ’yar shekaru 109 saboda ƙin bin dokar tsafta

Spread the love

Gwamnatin Jihar Abiya ta kama wata tsohuwa mai shekaru 109, Chidinma Eluwa, wadda ke sana’ar suyar ƙosai, bisa zargin karya dokar gudanar da aikin tsabtace muhalli na wata-wata a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa an kama Eluwa ne a ranar Asabar yayin da take suyar ƙosai a kan titin Owerri Road a lokacin da aka ware domin gudanar da aikin tsaftace muhalli. Daga bisani kuma aka gurfanar da ita a gaban Kotun Tsabtace Muhalli tare da wasu mutane 65 da ake zargi da irin wannan laifi.

Sai dai Alƙalin Kotun, Mai Shari’a O. C. Ibekwe, ya sallame ta bisa la’akari da tsufanta da kuma dalilan jinƙai.

Bayan samun ’yanci, tsohuwar ta yi alƙawarin bin dokokin tsaftace muhalli na jihar a nan gaba.

Daga cikin mutane 66 da aka gurfanar, kotun ta sallami mutum bakwai saboda matsalolin lafiya da kuma wasu dalilan da suka shafi ɗalibai, yayin da aka yanke wa mutum tara hukuncin yin aikin hidimar al’umma.

A halin da ake ciki, gwamnatin jihar ta yi gargaɗin cewa za ta iya ɗaukar tsauraran matakai wajen tabbatar da bin dokar tsaftace muhalli na wata-wata, bayan da ta lura da ƙarancin biyayya daga mazauna jihar.

Da yake jawabi bayan kammala aikin tsaftace muhalli na ranar Asabar, Kwamishinan Muhalli na Jihar Abiya, Philemon Ogbonna, wanda Shugabar Sashen Kula da Yawan Jama’a da Lafiyar Muhalli, Misis Happiness Akpulonu, ta wakilta, ya nuna damuwa kan yadda jama’a suka yi watsi da aikin.

Ya ce dakatar da aikin tsabtace muhalli na tsawon watanni da dama ya jawo taruwar shara a wurare da dama, musamman a Kasuwar Orie Ugba da wasu manyan kasuwannin jihar.

A cewarsa, jami’an tsaftace muhalli sun gamu da ƙalubale wajen kwashe ɗimbin sharar da ta taru.

“Mun fuskanci babban aiki. Tawagata ba ta iya kwashe dukkan sharar da aka tara ba. Mazauna Umuahia musamman sun fi mayar da martani idan an ɗauki matakan tilasta bin doka fiye da nasiha. Wataƙila lokaci ya yi da za mu rage nasiha mu aara aiwatar da doka,” inji shi.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga shugabannin ƙananan hukumomi da su wayar da kan jama’a tare da ƙarfafa sa ido kan ayyukan tsaftace muhalli a yankunansu.

Shi ma Shugaban Kwamitin Muhalli na Majalisar Dokokin Jihar Abiya kuma ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Ohafia ta Kudu, Kalu Mba-Nwoke, ya danganta ƙarancin halartar aikin da dakatar da shi na tsawon watanni uku.

Ya buƙaci jama’a su riƙa ɗaukar tsafta a matsayin alhakin yau da kullum maimakon jiran ranakun da gwamnati ta ware kawai.

“Tsabtace muhalli ya kamata ya kasance aiki na kullum. Ko ba tare da umarnin gwamnati ba, wajibi ne mu kula da muhallinmu saboda alhakinmu ne,” inji shi.

A nasa ɓangaren, Shugaban Al’ummar Arewa a Jihar Abiya kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa a yankunan Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas, Alhaji Yaro Danladi, ya sake jaddada goyon bayan al’ummarsa ga shirin tsaftace muhalli na wata-wata.

Ya bayyana cewa membobin al’ummar Arewa sun shiga aikin tsaftace muhalli domin nuna goyon baya ga manufofin gwamnati na kare muhalli da kuma samar da ingantacciyar rayuwa ga jama’a.

By ukarofi

Leave a Reply