Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Zartarwa ta Tarayyar Nijeriya (FEC), ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta amince da gudanar da garambawul ga tsarin Hukumar Kula da Matasa Masu Yi Wa ƙasa Hidima (NYSC).
Ministan Harkokin Matasa, Ayodele Olawande, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Litinin, 29 ga watan Yuni, 2026.
Olawande ya bayyana cewa an amince da sake fasalin NYSC ne a taron Majalisar Zartarwa da aka gudanar a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Litinin.
A cewarsa, garambawul ɗin zai haɗa da cikakken nazari kan yadda shirin NYSC ke gudana domin ya dace da buƙatun Nijeriya na yanzu.
Bayanai sun nuna cewa an kafa shirin NYSC ne a shekarar 1973 domin ƙarfafa haɗin kan ƙasa bayan yaƙin basasa da Nijeriya ta fuskanta.
Tsawon shekaru 53, shirin ya kasance wata hanya ta haɗa sababbin ɗaliban da suka kammala jami’a daga sassa daban-daban na ƙasar tare da bunƙasa zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al’umma.
Sai dai ministan ya ce bayan shafe shekaru da dama ana gudanar da shirin, ya zama wajibi a sake duba tsarin saboda sauye-sauyen da suka faru a ƙasar.
Olawande ya ce: “Buƙatun ƙasarmu sun sauya, kuma mutane da dama suna sa ran manufofin NYSC su ma su sauya domin su dace da halin da ake ciki a yanzu.”
Olawande ya bayyana cewa garambawul ɗin zai bai wa gwamnati damar tantance ko manufofi da tsarin gudanar da NYSC har yanzu suna biyan buƙatun ƙasa.
Sai dai bai bayyana cikakken bayani kan sauye-sauyen da za a aiwatar ko lokacin da za a fara aiwatar da garambawul ɗin ba.
Sauye-sauyen da aka yi wa NYSC:
1. Tsarin tura matasa garuruwan bauta da ya dogara da fasaha.
2. La’akari da barazanar tsaro wajen tura matasa domin kare masu yi wa ƙasa hidima.
3. Sabon tsarin zama a sansanin NYSC na tsawon makonni shida da zai maida hankali wajen koyar da harkar shugabanci, kasuwanci, ilmin fasahar zamani.
4. Amfani da ƙwarewa wajen tura jama’a wurin aiki daidai da ilimin da aka karanta da kuma tafarkin aiki.
5. Shugabanci na zamani a tsarin mulkin farar hula yayin da sojoji za su cigaba gudunmuwar tsaro.
6. Inganta sansanin hidimar ƙasa ta hanyar kawo tsarin tantancewa da auna tsarin a faɗin ƙasa.
7. Sabon tsarin biki da zai canji shirin yaye matasa da kuma kaki da aka sabunta waɗanda za su yi daidai da sanin aiki da kishin ƙasa.
