Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Alhaji Abdullahi Muhammad Gudale sakataren ƙungiyar Miyetti Allah ƙaramar hukumar Augie ya yi kira ga Fulani da su kai yaran su makaranta.
Ya yi wannan kira ne ranar Talatar da ta gabata a garin Augie yayin wani taron shugabannin Fulani da jami’an ƙaramar hukumar.
Ya bayyana cewa yanzu haka duk makarantun da aka gina domin yaran Fulani suna nan suna komawa kufai saboda rashin ɗalibai.
Yanzu haka malamai sun daina zuwa sanadiyyar ba kowa duk da ya ke a kowane wata gwamnati tana biyan su albashi.
Sanin kowa ne fulani mutane ne masu basira sosai da saurin ɗaukar ilmi kowane iri.
Ya ce lokacin jahiliyya ya wuce yanzu an shigo wani ƙarni na ya zama wajibi ga kowa ya kasance yana iya rubutawa da karantawa.
Gwamnati ta kashe maƙudan kuɗi ta shiga har cikin jeji ta gina makarantu domin ilmantarda Fulani saboda haka ba za mu bari a yi hasarar kuɗin a banza ba.
Za mu haɗa hannu da hukumar ilmi don ɗaukar duk matakin da ya dace ga duk wanda ya ƙi kai yaran sa makaranta. “Inji shi
