
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Zaman Majalisar Wakilai na ranar Laraba ya ɗauki wani ao bayan ‘ya’yanta sun shiga halin tayar da jijiyan wuya akan shawarar neman gayyatar Shugaba Bola Tinubu ya je ya yi bayanin zargin jinkirta aiwatar da Dokar Kasafi ta 2025.
Hakan ya biyo bayan da Ɗan majalisa Benedict Etanabene (Jihar Delta) ya yi tsokaci akan takardar umarnin da Akanta Janar na Ƙasa Shamseldeen Ogunjimi ya fitar.
A takardar da aka umarci saƙonta ya fara aiki daga ranar 29 ga Yuni, an umarci baki ɗaya ma’aikatu, cibiyoyi da hukumomin tarayya da su dakatar da biyan kuɗaɗen manyan ayyukan shiyyoyi da mazaɓu har sai an yi nazari kuma an tantance su daga ɓangaren Ma’aikatar Ayyuka na Musamman da Harkokin Gwamnatoci.
A cewar ɗan majalisar, matakin zai haifar da jinkirin aiwatar da ayyukan da aka sanya su cikin kasafi da kuma sanya ‘yan majalisa cikin mawuyacin hali na rashin aiwatar da ayyukan ci-gaba a mazaɓunsu.
Ya bayyana cewa, takardar ta gabatar da ƙarin sharaɗin gudanarwa da ba a sanya ba a Dokar Kasafi, yana mai gargaɗin hakan zai iya haddasa jinkiri wajen aiwatar da kasafin ƙasa.
Akan haka ne ya yi kira ga majalisar da ta gayyaci Shugaba Tinubu domin ya bayar da bayani akan jinkirin aiwatarwar da kuma hikimaf da ta sanya aka fitar da sabon umarnin, yana mai cewa al’umma da Majalisar Dokokin Ƙasa suna da haƙƙin a bayyana musu da gaskiyar al’amari akan batun.
Saidai, waɗannan kalamai sun haifar da saɓanin ra’ayoyi acikin ‘ya’yan majalisar yayin da wasu suka ƙi amincewa, wasu kuwa sun nuna goyon bayansu ga buƙatar gayyato shugaban.
