Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
‘Yan sanda a Katsina sun kai malamin jami’a, Dr Bashir Kurfi kotu bisa zargin yiwa Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa karya da ɓata suna.
Lauyan wanda ake ƙara Barista AD umar ya bayyana cewa kotu ta gabatar da tuhuma biyu da ake zargin Dr Kurfi da aikatawa wanda ya musanta.
Lauyan ya ce yau ne zaman na farko inda suka nemi bada belin wanda ake zargi tunda laifin bai kai matsayin da za a hana beli ba ne.
Sai dai a cewar sa ‘yan sanda masu gabatar da ƙara sun nuna rashin yarda da bada belin wanda ake zargi domin suna cigaba da bincike.
Barista AD umar ya bayyana cewa kotun bayan da ta saurari ɓangarorin biyu sai ta umurci ‘yan sanda su cigaba da riƙe wanda ake zargi har zuwa ranar Litinin don cigaba da shari’ar.
Kwanan baya ne a wata hira da wata kafar yada labarai Dr Bashir Kurfi ya yi zargin gwamnatin Dikko Raɗɗa ta ɗauki nauyin wasu ‘yan bindaga zuwa aikin hajji,zargin da gwamnati ta musanta.
