
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa akwai yiwuwar ba zai kasance a raye ba har zuwa zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Obi ya yi wannan furuci ne yayin wata hira da aka wallafa a shafin X na mai gabatar da shirye-shirye, Chude Jideonwo, inda ya zargi Gwamnatin Tarayya da hana shi gudanar da harkokinsa tare da matsa lamba akan ‘yan adawa.
Ya bayyana cewa, yana fuskantar cikas a kusan dukkan abubuwan da yake yi, inda ya yi zargin gwamnati na taka rawa wajen hana shi wasu hakkokinsa, duk da cewa bai gabatar da hujjojin da ke tabbatar da zarge-zargen ba.
Haka kuma, ya ce ya taɓa fuskantar matsala a wani filin jirgin sama inda aka kulle motarsa, yana mai ƙarawa da cewa wasu mutane na guje wa gaishe shi a bainar jama’a saboda tsoron abin da ka iya biyo baya.
Har ila yau, ya yi zargin cewa wasu daga cikin magoya bayansa kan roƙe shi kada ya halarci bukukuwan iyalansu saboda tsoron abin da hakan ka iya jawo musu.
Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, Gwamnatin Tarayya ba ta mayar da martani akan zarge-zargen da ɗan takarar shugaban ƙasar ya yi ba.
