An tsare lakcara a Katsina bayan zargin gwamnatin jihar da ɗaukar nauyin aikin hajjin wasu manyan ‘yan bindiga

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Babbar Kotun Shari’a da ke Katsina ta ba da umarnin tsare Dr. Bashir Kurfi, malami a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, bayan rundunar ‘yan sandan Jihar ta gurfanar da shi bisa zargin vata suna da kuma yaxa bayanan qarya masu tayar da hankali kan gwamnatin jihar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito ‘Yan sanda sun ce Dr. Kurfi ya yi iqirarin a wata hira da ya yi a Trust TV cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta xauki nauyin wasu ‘yan bindiga zuwa aikin Hajji, zargin da gwamnati ta musanta.

Bayan ya musanta laifukan da ake tuhumarsa da su, lauyansa ya nemi a ba shi beli, amma kotu ta umarci a ci gaba da tsare shi a hannun ‘yan sanda tare da ci gaba da bincike.

Kotun ta xage sauraron shari’ar zuwa ranar 14 ga Yulin, 2026.

Idan za a iya tunawa Blueprint Manhaja ta rawaito cewa ‘yan kwanaki bayan da Dr. Kurfi ya zargin gwamnatin jihar Katsina da biya wa ‘yan ta’adda aikin hajji, sai ga wasu rahotanni sun fito inda Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa jami’an DSS sun kama wasu da ake zargin shugabannin ‘yan bindiga ne yayin da suke dawowa daga aikin Hajji a Filin Jirgin Sama na Umaru Musa Yar’Adua dake Katsina.

By Babaji

Leave a Reply