Injiniya Rabi’u ya raba takin zamani buhu 200 ga al’ummar yankin Burdugau a Katsina

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Al’ummar garin Burdugau da ke ƙaramar hukumar Malumfashi a Jihar Katsina da al’ummomin da ke kewaye da su sun yaba da wani mai taimakon al’umma, Injiniya Muhammad Rabi’u Hashim, bayan gudanar da babban taron tallafawa ga manoma, mata masu aure, da kuma marasa lafiya a yankin.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a madadin al’umma, mazauna yankin sun bayyana godiyarsu bisa wannan alheri da suka ce ya zo daidai lokaci kuma ya yi tasiri ga rayuwar alummar yankin.

A cewar al’ummar, Injiniya Rabi’u Hashim ya bayar da buhunan taki guda 200 kimani Naira miliyan 12 ga manoman Burdugau G kyauta.

An raba takin kyauta domin ƙara haɓaka harkar noma a wannan damina da muke ciki.

Baya ga tallafin noma, Injiniya Rabiu ya kuma bai wa mata masu aure tallafin kuɗi N200,000 a cikin al’ummar garin Burdugau.

Don tallafawa buƙatun lafiya, Injiniya Hashim ya ƙara bayar da buhunan shinkafa bakwai ga marasa lafiya a Burdugau da kewaye.

Shugabannin al’umma sun bayyana tallafin a matsayin abinda ya shafi muhimman fannoni na buƙata kamar abinci, tallafin gida, da lafiya, inda suka ce zai kawo sauƙin kai tsaye ga gidajen da ke cikin mawuyacin hali.

Da yake jawabi a madadin al’ummar Burdugau, Sanusi Muhammad ya ce tallafin ya nuna jajircewa ga ci gaban al’umma da rage talauci.

“Mutanen Burdugau da yankunan da ke kewaye da su na godiya kuma muna addu’a fatan alkhairi ga Injiniya ya Rabiu Hashim” in ji Sanusi Muhammad.

Al’ummar sun yi addu’o’i na musamman ga Injiniya Rabiu Hashim, suna roƙon “Allah ya ci gaba da ɗaga shi, ya ƙara masa albarka a cikin dukiyarsa.”

Wannan tallafi ya zo ne a lokacin da farashin kayan aikin gona ke ci gaba da zama babban matsala ga al’ummomin karkara a faɗin Jihar Katsina.

Masu ruwa da tsaki sun ce bayar da taki da tallafin kuɗin kai tsaye ga mata yana da matuƙar muhimmanci wajen taimaka wa iyalai wajen ci gaba da noma da biyan buƙatunsu na yau da kullum.

Mazauna yankin sun ce suna fatan wannan alheri zai ƙarfafa sauran mutanen da ke da niyya mai kyau su saka hannu wajen ci gaban al’ummomin su.

By ukarofi