Kotu ta umarci a ƙwace kadarorin biliyan N212.8 da aka alaƙanta da Malami na dindindin

Spread the love

Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, ta bayar da umarnin ƙwace sama da kadarori guda 40 da ake danganta su da tsohon Antoni Janar na Kasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, tare da mayar da su mallakin Gamnatin Tarayya.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta yanke hukuncin a ranar Laraba, bayan ta amince da buƙatar Hukumar EFCC, wadda ta ce Malami da sauran masu iƙirarin mallakar kadarorin sun kasa tabbatar wa kotu cewa sun mallake su ne ta hanyoyin da doka ta aminta da su.

Gabanin hukuncin, kotun ta yi watsi da duk ƙorafe-ƙorafe da buƙatun da Malami, iyalansa da wasu kamfanoni da ke ikirarin mallakar kadarorin ne suka gabatar, inda ta ce ta yi haka ne domin ba su da asali.

Mai shari’ar ta bayyana cewa abin da kotun ke dubawa ba wai waye ya mallaki kadarorin ba ne, sai dai ko kuɗin da aka yi amfani da su wajen sayen kadarorin sun fito ne ta halastacciyar hanya.

Ta ce, waɗanda ake ƙara sun kasa kawar da zargin da EFCC ta gabatar cewa an mallaki kadarorin ne ta haramtattun hanyoyi.

Kotun ta jaddada cewa, ƙwace kadarorin ba ya nufin an samu Malami ko wani da laifi a shari’ar aikata laifi, domin har yanzu Malami, matarsa da ɗansa na fuskantar shari’ar zargin halasta kuɗaɗen haram da ta kai biliyan N8.7.

By Babaji

Leave a Reply