Majalisar Dattawa za ta fara bin diddigin hazaƙar wakilai yayin kowane zama

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Dattawa na shirin samar da wani tsari domin kula da lamuran halarta da hazaƙar sanatoci a yayin zaman majalisa, a matsayin wani ɓangare na ƙarfafa ƙoƙarinsu a harkokinta.

Sanata Abdul Ningi (Jihar Bauchi) ne ya gabatar da buƙatar a ranar Laraba, inda nemi shugabancin majalisar da ta riƙa tattara rahoton halarta da gudunmawa yayin muhawara akan muhimman batutuwan majalisa.

A cewarsa, yana da kyau a riƙa tantance wa da wa ne suke ƙoƙarin bayar da gudunmawa a majalisar domin ƙara wa mambobin ƙwarin-gwiwar tofa albarkacin baki da yin abin da ya dace akan batutuwan da ake gabatarwa domin tattauna su.

Ya ce, ajiye rahoton hakan zai taimaka wajen inganta ayyukan majalisa da ƙarfafa shawarwari yayin muhawara a babban zauren.

Wannan buƙata ta samu goyon baya daga sanatoci da dama, inda wasu ma har kira suke da a riƙa bayar da kyautar karramawa ga waɗanda suka fi bayar da gudunmawa.

By Babaji

Leave a Reply