Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Kungiyar ’yan kasuwar Yankaba da ke sana’ar sayar da kayan miya a Jihar Kano ta roƙi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya saka mambobinta cikin shirin tallafin jari na wata-wata da gwamnatin jihar ke gudanarwa domin bunƙasa kasuwanci.
Shugaban ƙungiyar, Alhaji Rabiu A. Danladi, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da wakilin Manhaja a ofishinsa da ke kasuwar a ranar Lahadi.
Ya ce yawancin ’yan kasuwar, musamman masu ƙaramin jari, na fuskantar ƙalubale sakamakon tsadar rayuwa da ake fama da ita a halin yanzu.
A cewarsa, saka mambobin ƙungiyar cikin shirin tallafin zai taimaka musu matuƙa wajen faɗaɗa harkokinsu da inganta rayuwarsu.
Ya kuma bayyana cewa ’yan kasuwar Yankaba a shirye suke su ci gaba da bai wa gwamnati cikakken goyon baya wajen aiwatar da shirye-shiryenta na ci gaban jihar.
Hakazalika, ya yaba wa Shugaban ƙaramar Hukumar Nasarawa, Hon. Yusuf Imam Ogan Boye, bisa gudummawar da yake bayarwa wajen bunƙasa kasuwar da inganta harkokin kasuwanci a yankin.
Ya kuma yi kira ga ’yan kasuwar da su ci gaba da yi wa gwamnatin Abba Kabir Yusuf addu’ar samun nasara da kuma ci gaba da aiwatar da manufofin ci gaba.
A nata ɓangaren, shugabar mata ta kasuwar, Malama Abasiya Mujidtapha, ta bayyana cewa mata ne suka fi rinjaye a cikin masu gudanar da kasuwanci a Yankaba, kuma da dama daga cikinsu su ne ke ɗaukar nauyin iyalansu da marayu.
Ta ce yawancin matan na fuskantar matsalar rashin isasshen jari, lamarin da ke kawo cikas ga bunƙasar kasuwancinsu.
Saboda haka, ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta duba wannan buƙata domin tallafa wa mata ’yan kasuwa da jari da zai taimaka musu wajen bunƙasa sana’o’insu.
