Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da cibiyar sarrafa rogo da gari a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ƙaddamar da sabuwar cibiyar sarrafa rogo da gari a ƙaramar hukumar Batsari, tare da sanya mata sunan marigayi tsohon ministan noma da albarkatun ruwa, Dr. Abba Sayyadi Ruma, domin girmama gudummawar da ya bayar.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa cibiyar wani muhimmin mataki ne na cika alƙawarin gwamnatinsa na bunƙasa noma, samar da ayyukan yi, rage talauci da ƙarfafa tattalin arzikin karkara.

Ya ce gwamnati ta himmatu wajen mayar da noma kasuwanci mai riba ta hanyar sarrafawa, adanawa, tattarawa da samar da kasuwanni.

Ya ce cibiyar za ta taimaka wajen rage asarar amfanin gona bayan girbi, samar da kasuwa ga manoma, ƙara kuɗaɗen shiga, da samar da ayyukan yi ga matasa da mata.

Babban daraktan hukumar KASEDA, Dr. Babangida Kabir Ruma, ya ce cibiyar za ta ƙarfafa darajar rogo tare da inganta sana’o’in karkara da samar da arziki.

Ya buƙaci manoma, kungiyoyin mata da matasa su kula da cibiyar tare da amfani da ita yadda ya kamata.

Mataimakin gwamna, Malam Faruk Lawal Joɓe, da shugaban ƙaramar hukumar Batsari, Hon. Mannir Mu’azu, sun yaba wa Gwamna Raɗɗa bisa wannan gagarumin aikin da suka ce zai bunƙasa tattalin arzikin yankin tare da inganta rayuwar al’umma.

An gudanar da bikin ne tare da halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, ‘yan majalisar jiha, abokan hulɗar ci gaba, manoma, ƙungiyoyin mata da matasa, da sauran masu ruwa da tsaki.

By ukarofi

Leave a Reply