Sojoji sun daƙile yunƙurin Boko Haram na tatsar kuɗi daga jama’a a Yobe

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun daƙile wani yunƙuri da mayaƙan Boko Haram/ISWAP suka yi na tatsar kuɗi daga al’ummomi a Jihar Yobe ta hanyar karɓar haraji ba bisa ka’ida ba.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce bayanan sirri da dakarun suka samu sun nuna cewa ‘yan ta’addan na amfani da wasu motoci da babura wajen tattara kuɗaɗe daga fararen hula a yankin.

Rundunar ta ce bayan samun bayanan sirrin, dakarunta suka gudanar da sintiri na musamman a yankin Paya Kafiya ranar 19 ga Yulin 2026.

Bayan sun yi arangama da ‘yan ta’addan, sojojin suka buɗe musu wuta, inda suka lalata ɗaya daga cikin motocinsu tare da kashe direban motar.

Rundunar ta ƙara da cewa wasu ‘yan ta’adda huɗu sun tsere zuwa cikin daji da raunukan harbin bindiga.

A wani samame da sojojin saka ci gaba da yi ranar 20 ga Yuli, sun yi nasarar ƙwato makammai da harsasai da wata mota..

Rundunar ta ce nasarar ta taimaka wajen tarwatsa hanyoyin samun haramtattun kuɗaɗen Boko Haram/ISWAP a Arewa maso Gabashin Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply