Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya), ya buƙaci a riƙa yi wa masu shirin aure da kuma ɗaliban da ke neman shiga manyan makarantu gwajin miyagun ƙwayoyi domin daƙile yaɗuwar shaye-shaye.
Marwa ya bayyana hakan ne a Dutse yayin ƙaddamar da yaƙin neman kawar da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da farfaɗo da kyawawan ɗabi’u.
Ya ce kamar yadda ake yin gwajin cutar HIɓ da na ƙwayoyin halitta (genotype) kafin aure, ya kamata a haɗa da gwajin miyagun ƙwayoyi.
A cewarsa, babu wani uba ko uwa da zai so aurar da ‘yarsa ga mai shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa yin irin wannan gwaji zai taimaka wajen rage matsalolin da shaye-shaye ke haifarwa a gidajen aure.
Marwa ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da yin gwajin miyagun ƙwayoyi ga ɗaliban manyan makarantu kafin su fara karatu domin rage yawan masu faɗawa shaye-shaye.
Ya ce shaye-shaye na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa rashin tsaro, ta’addanci, rugujewar tattalin arziki da kuma tarwatsewar iyalai, yana mai jaddada cewa magance matsalar na buƙatar haɗin kan iyaye, malamai, sarakuna, shugabannin addini, ƙungiyoyin al’umma da hukumomin tsaro.
Marwa ya ce daga Janairun 2021 zuwa Disamban 2025, NDLEA ta kama mutum 77,859 da ake zargi da aikata laifukan miyagun ƙwayoyi, ta samu hukuncin kotu kan mutum 14,122, tare da ƙwace miyagun ƙwayoyi masu nauyin kilogram miliyan 14.8.
Ya kuma ce sama da mutum 50,000 sun samu kulawa da jinya a cibiyoyin gyaran masu shaye-shaye na hukumar, yayin da bincike ya nuna cewa masu amfani da miyagun ƙwayoyi a Jihar Jigawa sun kai kashi bakwai cikin ɗari, adadin da ke cikin mafi ƙanƙanta a ƙasar.
Marwa ya yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa goyon bayan da yake bai wa NDLEA, yana mai cewa babu wani gwamna da ya bai wa hukumar tallafi a jiharsa fiye da shi.
A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya ce dokokin zartarwa guda biyu da ya sanya wa hannu na daga cikin matakan ƙarfafa yaƙi da shaye-shaye da inganta kyawawan ɗabi’u a jihar.
Ya buƙaci iyaye, shugabannin addini da na gargajiya, malamai da sauran masu ruwa da tsaki su mara wa shirin baya domin kare matasa daga illolin miyagun ƙwayoyi.
