Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Haraji ta Nijeriya (NRS) ta sanya ranar 31 ga Yuli, 2026 a matsayin wa’adin ƙarshe da dukkan manyan masu biyan haraji za su kammala komawa tsarin e-Invoicing da kuma Tsarin Lissafin Kuɗi na Fasahar Zamani (EFS).
Matakin ya biyo bayan sanarwar da hukumar ta fitar tun ranar 17 ga Fabrairu, 2026, wadda ta bayyana jaddawalin aiwatar da sabon tsarin tare da wajabta amfani da shi. Ana kuma kiran tsarin da suna ‘Merchant Buyer Solution’ (MBS).
Shugaban Hukumar Kula da Haraji ta Nijeriya, Zacch Adedeji, ne ya sanya hannu kan sanarwar, inda ya umarci dukkan manyan masu biyan haraji da su kammala rajista, haɗa tsarin kamfanoninsu da na hukumar, gudanar da gwaje-gwajen da suka dace, sannan su fara tura takardun rasit da bayanan ciniki zuwa dandalin e-Invoicing na NRS bisa ƙa’idojin da aka tanada.
A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Hukumar Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Dare Adekanmbi, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce NRS ta fara sa ido kan yadda manyan kamfanoni ke bin sabon tsarin domin tantance matakin biyayyarsu.
Sanarwar ta yi gargaɗin cewa duk wani kamfani da ya kasa bin umarnin kafin wa’adin zai iya fuskantar matakan ladabtarwa da hukuncin da dokokin haraji da ƙa’idojin da suka dace suka tanada.
Saboda haka, hukumar ta buƙaci dukkan kamfanonin da abin ya shafa da su gaggauta kammala duk wasu matakan rajista da haɗa tsarin bayanansu da na hukumar, tare da fara aika takardun rasit ta hanyar lantarki kafin ranar ƙarshe.
NRS ta kuma bayyana godiyarta ga masu biyan haraji bisa haɗin kan da suke bayarwa, tana mai tabbatar da cewa za ta ci gaba da ba su dukkan tallafin da ya dace domin tabbatar da nasarar aiwatar da sabon tsarin e-Invoicing a faɗin ƙasar.
A cewar hukumar, manyan masu biyan haraji su ne kamfanonin da ke samun kuɗaɗen shiga na Naira biliyan biyar ko sama da haka a shekara. Zuwa ƙarshen zangon farko na shekarar nan, fiye da kamfanoni 1,000 sun riga sun cika sharuɗɗan tsarin.
Domin cika ƙa’idojin tsarin, ana buƙatar kamfanoni su kammala rajista a dandalin Merchant Buyer Solution (MBS) na NRS, su haɗa tsarin bayanansu ta hanyar amincewar Masu Ba da Sabis na Access Point Providers (APPs) ko Masu Haɗa Tsarukan Bayanai (SIs).
Haka kuma, dole ne su kammala dukkan gwaje-gwajen da ake buƙata, su fara aika takardun rasit zuwa dandalin e-Invoicing na NRS bisa ƙa’idojin da aka amince da su, tare da tabbatar da cewa suna karɓar rasit na lantarki da ke ɗauke da Lambar Shaidar Rasit (RIN) daga masu samar musu da kayayyaki ko ayyuka.
