Kotu ta yanke wa wani hukuncin kisa ta hanyar rataya kan kashe mata mai ciki a Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Babbar kotun Jihar Kano ta yanke wa wani mutum mai suna Shuaibu Abdulkadir hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same shi da laifin kashe wata mata mai juna biyu mai suna Rumaisa Shuaibu.

Mai shari’a Farida Rabiu-Danbappa ta kotun mai lamba 22 da ke kan titin Miller a Kano ce ta yanke hukuncin a ranar Juma’a, bayan ta tabbatar da cewa an same shi da laifin kisan kai da gangan, laifin da sashe na 221 na kundin dokokin hukunta laifuka ya tanadar wa hukuncin kisa.

Mai shari’ar ta bayyana cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifin da ake tuhumar wanda ake zargi da shi ba tare da wata shakka ba.

Ta ce, ” Shuaibu Abdulkadir na sameka da laifin kisan kai da gangan. Saboda haka, na yanke maka hukuncin kisa ta hanyar rataya. Allah ya jiƙanka. Kana da damar ɗaukaka ƙara cikin kwanaki 90.”

Lauyan gwamnati mai gabatar da ƙara, Basiru Aliyu, ya shaida wa kotu cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya kashe marigayiyar mai shekara 22, wadda ke ɗauke da juna biyu a lokacin, a gidanta da ke unguwar Farawa, cikin ƙaramar hukumar Kumbotso ta Jihar Kano, a shekarar 2025.

A cewar masu gabatar da ƙarar, kafin aukuwar lamarin marigayiyar ta nemi wanda ake tuhuma ya biya ta kuɗin da ake zargin yana bin ta. Daga nan ne ya ɗaure mata wuya, sannan ya yanke mata maƙogwaro da wuka mai kaifi, lamarin da ya yi sanadin rasuwarta.

Kotun ta kuma ji cewa marigayiyar ƙawar wadda ake shirin aura wa wanda aka yanke wa hukuncin ce.

Domin tabbatar da tuhumar, masu gabatar da ƙarar sun gabatar da shaidu uku, waɗanda suka haɗa da mijin marigayiyar Ibrahim Muhammad, budurwar wanda ake tuhuma Asiya Abdulmalik, da jami’in ‘yan sanda mai binciken lamarin, ASP Chindo Chiwa.

Kazalika, sun gabatar da hujjoji daban-daban da suka haɗa da rubutacciyar amsa laifin da wanda ake tuhuma ya yi, faifan bidiyo, hujjojin na’ura mai kwakwalwa, hotunan marigayiyar, wukar da ake zargin an yi amfani da ita wajen kisan, da kuma wayar salular wanda aka yanke wa hukuncin.

A nasa ɓangaren, Shuaibu Abdulkadir ya musanta aikata laifin, inda ya ba da shaidarsa a gaban kotu. Lauyansa, Mustapha Idris, ya roƙi kotun ta yi masa sassauci, yana mai cewa wannan ne karo na farko da ya aikata irin wannan laifi, kuma ya nuna nadama.
Sai dai bayan nazarin dukkan hujjojin da aka gabatar, Mai shari’a Farida Rabiu-Danbappa ta same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

By ukarofi

Leave a Reply