
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An zargin wasu jami’an hukumar ‘yan sandan ƙasar Afirka ta Kudu (SAPS) da halaka wani ɗan Nijeriya mai suna Mista Chika Ibe a lokacin da suke gudanar da atisaye a yankin Parksig Villas da ke Belleville a Birnin Cape Town.
Rahotanni sun bayyana cewa, Ƙungiyar ‘yan Nijeriya mazauna ƙasar (NICASA) ce ta bayyana haka, inda ta yi alla-wadai da mummunan kisan ɗan Nijeriyar, inda ta yi kira da a gaggauta gudanar da bincike akan al’amarin.
A cewar NICASA, Mista Ibe, wanda ɗan yankin Lokpaukwu na Jihar Abia ne, ya haɗu da ajalin nasa ne a lokacin aka lakaɗa masa yayin jami’an suke atisaye.
Shugaban NICASA, Rev. Frank Onyekwelu ya ce matuƙar aka tabbatar da zargin, to hakan taka dokar ‘yancin ɗan-adam ne da na shari’a.
Don haka ne ƙungiyar ta yi kira ga cibiyar bincike na ‘yan sanda (IPID) da jagorancin hukumar ‘yan sandan ƙasar da su gaggauta ƙaddamar da bincike kai cike da gaskiya da adalci akan al’amarin.
NICASA ta kuma ci alwashin cewa dukkan wani jami’in da aka samu da hannu a ɗanyen aikin, zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada.
