Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta kafa masana’antun sana’o’in hannu, wato Cottage Industry, da cibiyoyin kasuwanci, wato Cottage Enterprise Hubs, a muhimman sassan jihar domin haɓaka masana’antu, ƙarfafa samar da kayayyakin cikin gida da kuma samar da ayyukan yi ga matasa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin shirin tallafa wa mahauta da suka yi rajista, wanda Hukumar Kasuwancin Cottage ta Jihar Kano (CTSHA) ta shirya a Gidan Gwamnatin Kano.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a, an bayyana cewa an tanadi aikin ne a cikin kasafin kuɗin Jihar Kano na shekarar 2026 da aka amince da shi.
Gwamna Yusuf ya ce cibiyoyin da ake shirin kafawa za su kasance cibiyoyin samar da kayayyaki na zamani ga masu sana’o’in hannu da ƙananan ’yan kasuwa. Ya ce za su samar da wuraren aiki na bai ɗaya, na’urori na zamani, ingantattun kayan more rayuwa, wuraren ajiya, tallafin gudanar da kasuwanci, horas da sana’o’i da kuma hanyoyin kai kayayyaki kasuwa cikin tsari.
Ya bayyana cewa manufar shirin ita ce ƙara yawan samar da kayayyaki, inganta gasa tsakanin masana’antun cikin gida da kuma rage kuɗaɗen gudanar da kasuwanci ga masu sana’o’i.
Gwamnan ya ce shirin ya yi daidai da Ajandar Sabunta Fat, wato Renewed Hope Agenda ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wadda ke ƙarfafa samar da kayayyakin da aka ƙera a Nijeriya da kuma amfani da su.
Haka kuma, ya ce yana tafiya daidai da Ajandar Kano First, wadda ke fifita bunƙasa kasuwanci da masana’antun ’yan asalin jihar tare da ƙarfafa tattalin arzikinta.
Ya ƙara da cewa, za a ware sassa na musamman a cikin cibiyoyin domin mahauta, masu sarrafa nama, masu sarrafa fata da masana’antun tanning, domin ƙarfafa sarkar darajar kiwo a jihar da kuma jawo ƙarin masu zuba jari zuwa wannan fanni.
A cewarsa, wannan shiri zai rage kuɗaɗen samar da kayayyaki, inganta ingancinsu, faɗaɗa kasuwanni tare da samar da dubban guraben aikin yi ga matasa a fannonin sarrafa nama, sarrafa fata, tattara kayayyaki, sufuri da sauran masana’antun da ke da alaƙa da su.
Gwamna Yusuf ya kuma buƙaci waɗanda suka amfana da shirin tallafin da su yi amfani da damar yadda ya kamata, su kiyaye tsafta da ƙwarewa a aikinsu, sannan su ƙarfafa sauran masu sana’o’in da suka cancanta su yi rajista da hukumar domin su ma su ci gajiyar shirye-shiryen gwamnati na gaba.
