
Ƙoƙarin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu yake yi na samar da tsaro a ko’ina cikin fadin Najeriya nata jan hankalin al’ummar duniya.
Kwanan nan ne Mista Donald Trump, Shugaban Kasar Amurka, ya jinjina wa Shugaba Tinubu kan nasarorin da yake samu wajen wanzar da zaman lafiya a Najeriya. Wannan alamar ce ga yan adawa su daina sukar gwamnati, su taho su hada hannu wajen samar da cikakken tsaro a fadin Nijeriya.
Wannan shine sakon Hon. (Dr) Musa Iliyasu Kwankwaso, Babban Daraktan Kudi da Gudanarwa na Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are, wanda ya sanya hannu aka rabawa yan jarida.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya ci gaba da cewa duk da yabon da Shugaba Tinubu ke samu, musamman na kwanan nan daga Shugaba Trump, hakan bai sa Shugaba Tinubu ya yi sakaci ba wajen kokarin ci gaba da samar da tsaro ta yadda yan kasa za su yi barci ba tare da wani fargaba ba.
“Za ku iya ganin yabo da jinjina da Shugaba Tinubu ke samu domin kokarin sa na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ko’ina cikin kasa. Saboda haka ne ma Shugaba Trump da kansa ya jinjinawa Shugaba Tinubu, wanda haka ke nuni da cewa Gwamnatin Tinubu na kan tafarkin kawo karshen rashin tsaro,” in ji shi.
Sannan, ya yi kira ga duk masu kishin kasa su ci gaba da marawa gwamnati baya domin samun nasarar kawo karshen rashin tsaro.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya kara da cewa wata shaida ta kokarin Shugaba Tinubu na samar da tsaro ita ce bada umarnin fadada rundunonin Sojoji a Nijeriya daga 8 zuwa 12.
A cewar Bayo Onanuga, Mataimakin na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai, a cikin wata sanarwa ga manema labarai, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin kara fadada rundunonin Sojoji daga takwas zuwa sha biyu, wanda hakan zai taimakawa ayyukan Sojojin Nijeriya.
A cewarsa, wannan umarnin na Shugaban Kasa na nuni da kokarin sa wajen samar da ingantattun hanyoyi da za su karfafa tsaron kasa.
Ya kuma yi wa ‘yan Nijeriya fatan cewa nan ba da jimawa ba yan kasa za su iya zirga-zirga a ko’ina cikin kasa ba tare da fargaban wani hari ba.
Babban Daraktan ya kuma jinjinawa Malam Nuhu Ribadu, da Ministocin Tsaro Musa da Matawalle, da dukkan Shugabanin rundunonin jami’an tsaro kan kokarin su wajen inganta tsaron Nijeriya.
A ƙarshe, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su cigaba da yi wa waɗannan jajirtattun jami’an tsaro addu’ar samun nasara wajen kawo karshen rashin tsaro a ko’ina cikin kasa.
