
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo da tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar, sun sabunta tsohon rikicin su na siyasa, yayin da suka fara musayar zarge-zarge akan zargin kitsa tsigewa da shirin neman wa’adi na uku da suka sanya dangantakarsu ta yi tsami.
Obasanjo ya zargi Atiku da ba wa tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na’Abba Naira miliyan 5 domin ya fara tsara shirin tsige shi tun a wa’adinsa na farko a matsayin shugaban ƙasa.
Tsohon shugaban ƙasar ya yi wannan zargi ne a lokacin da yake bayar da amsa game da kalaman tsohon gwamnan jihar Ogun, Olusegun Osoba akan al’amuran siyasar da suka faru gabanin babban zaɓen 2003.
Obasanjo ya bayyana cewa, Atiku ya samu Na’Abba a sirrance a fadar shugaban ƙasa, inda ya buƙaci da ya fara shirin tsige Obasanjo domin wa’adinsa ya taƙaita a ɗaya kaɗai.
Ya yi iƙirarin cewa, an shirya rahoton ganawa da biyan kuɗaɗen, wanda shugaban ma’aikatan fadarsa da ya bayyana a matsayin jami’in leƙen asiri ya gabatar masa.
Obasanjo ya ƙara da cewa, bai shiga damuwa ba akan batun kasancewar yana sane da cewa babu wata doka da ta bayar da damar tsige shi daga muƙamin.
Da yake martani akan kalaman ta bakin mai taimaka masa akan hulɗa da jama’a, Phrank Shaibu, Atiku ya yi watsi da zargin, inda ya ƙalubalance Obasanjo akan me ya sa sai bayan rasuwar Na’Abba sannan yake yin iƙirarin.
Ya bayyana cewa, tsohon kakakin ba ya raye ballanta ya tabbatar ko ya musanta zargin.
Kazalika, ya yi tambaya akan mai ya sa ba a ɗauki matakin shari’a ba akansa a lokacin muddin an samu hujjar da ke tabbatar da zargin.
A cewarsa, an fitar da zargin ne da nufin rage masa kima gabanin babban zaɓen 2027 da kuma bayar da dama ga ɗan takarar da Obasanjo ya fi so.
