Nijeriya ba za ta wadata ta hanyar karɓar bashi ko ƙara haraji ba – Atiku

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Dan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa Nijeriya ba za ta kai ga bunƙasar tattalin arziki ta hanyar ci gaba da karɓar bashi, shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje da kuma ƙara haraji ba.

Ya ce mafita ita ce ƙasar ta mayar da hankali wajen samar da abin da take ci, ƙera abin da take amfani da shi, sannan ta fitar da kayayyakin da take samarwa zuwa ƙasashen waje.

A cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Litinin, Atiku ya ce ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa ba zai samu ba sai an ƙarfafa samar da kayayyaki, bunƙasa masana’antu da kuma haɓaka fitar da kayayyakin cikin gida zuwa kasuwannin duniya.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce matsalolin tattalin arzikin Nijeriya ba wai na sauye-sauyen tattalin arzikin duniya kaɗai ba ne, illa kuma sakamakon manufofin da aka daɗe ana aiwatarwa waɗanda suka fi fifita amfani da kayayyaki maimakon samar da su.

A cewarsa, Nijeriya ta daɗe tana alfahari da shigo da kayayyaki daga ƙetare yayin da ta yi watsi da samar da su a gida. Ya ce, har yanzu ana shigo da abincin da ya kamata manoma a Nijeriya su noma, ana shigo da kayayyakin da ya dace masana’antun cikin gida su ƙera, har ma da albarkatun ƙasa da ya kamata a sarrafa su a cikin ƙasar.

Atiku ya jaddada cewa babu wata ƙasa da ta taɓa samun ci gaba ta hanyar fitar da ayyukan yi zuwa ƙasashen waje tare da shigo da talauci cikin gida. Ya yi nuni da hauhawar farashin abinci da kuma matsin da masana’antun Nijeriya ke fuskanta a matsayin hujjar cewa tsarin tattalin arzikin da ake bi a halin yanzu ya gaza.

A cewarsa, hauhawar farashin abinci a matakin ƙasa ta kai kashi 17.52, yayin da wasu jihohi ke fuskantar matsanancin hauhawar farashi, ciki har da Kogi mai kashi 53.02 da Neja mai kashi 43.83, lamarin da ya ce yana hana miliyoyin ‘yan Nijeriya samun isasshen abinci. Ya kuma bayyana cewa masana’antun Nijeriya sun kashe naira tiriliyan 3.53 wajen shigo da albarkatun ƙasa cikin watanni shida kacal, yana mai cewa raguwar harajin da masana’antun ke biya alama ce da ke nuna cewa ayyukan masana’antu na ci gaba da raguwa.

“Aiki ba zai bunƙasa ba idan masana’antu na ci gaba da rufewa. Muna fitar da ayyukan yi zuwa ƙasashen waje, muna shigo da hauhawar farashi, muna raunana darajar naira tare da jingina makomar ƙasar,” inji shi.

Atiku ya yi kira da a sake fasalin tattalin arzikin Nijeriya ta yadda zai ta’allaka kan noma, masana’antu, ma’adinai, fasaha da kuma ƙara darajar albarkatun cikin gida ta hanyar sarrafa su. Ya ce idan ana sarrafa kayan amfanin gona da sauran albarkatun ƙasa a Nijeriya, hakan zai samar da dubban ayyukan yi, ya ƙarfafa darajar naira tare da rage dogaro da kayayyakin waje.

Ya misalta da cewa duk buhun koko da aka sarrafa daga yankin Idanre da sauran sassan Jihar Ondo, duk buhun shinkafar da aka noma a Kebbi, doyan da aka shuka a Benuwe, tumatirin da aka sarrafa a Kano, magungunan da aka ƙera a Aba, kayan fata da aka samar a Kano da kuma injinan da aka haɗa a Nnewi, duk suna samar da ayyukan yi, suna ƙarfafa tattalin arziki tare da rage dogaro da shigo da kayayyaki.

Da yake waiwayar lokacin da yake cikin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, Atiku ya ce gwamnatin ta aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da suka dawo da kwarin gwiwar masu zuba jari, suka buɗe ƙofofin wasu manyan fannoni ga masu zaman kansu tare da jawo manyan jarin cikin gida da na waje, wanda ya kafa tubalin ɗaya daga cikin lokutan da tattalin arzikin Nijeriya ya fi ƙarfi.

Har ila yau, ya bayyana abubuwan da gwamnatin ADC za ta mayar da hankali a kai idan ta samu damar mulki a shekarar 2027. Ya ce, gwamnati za ta tabbatar da tsaro a yankunan noma da kuma wuraren masana’antu, yana mai cewa babu yadda za a samu wadatar abinci ba tare da tsaron manoma ba.

A cewarsa, manufofin da za su aiwatar sun haɗa da rage harajin shigo da injinan masana’antu da ba a ƙera su a Nijeriya, samar da rance mai sauƙi na dogon lokaci ga manoma da masana’antun cikin gida, tabbatar da farashin lantarki da man fetur mai sauƙi, daidaita darajar naira, saka hannun jari a fannin wutar lantarki, hanyoyi, layukan dogo, ban ruwa da wuraren adana amfanin gona.

Ya kuma ce za su bunƙasa cibiyoyin sarrafa amfanin gona da masana’antu, su gyara tsarin haraji domin ƙarfafa samar da kayayyaki, tare da tabbatar da ma’aikata sun samu albashi mai kyau domin ƙara ƙarfin sayen kayayyakin cikin gida.

Atiku ya ce, masana’antu ba za su iya bunƙasa ba idan kuɗin ruwa kan rance ya yi yawa, makamashi ya yi tsada, darajar kuɗi ba ta da tabbas kuma jama’a ba su da ƙarfin sayen kayayyakin da ake ƙerawa a cikin gida. Ya ce manufarsu ita ce a samar da kayayyaki a Nijeriya, a ɗauki ‘yan Nijeriya aiki, a amfani da kayayyakin da aka ƙera a gida, sannan a fitar da su zuwa ƙasashen duniya.

A ƙarshe, Atiku ya jaddada cewa arzikin kowace ƙasa ba ya ta’allaka kan yawan kayayyakin da take shigowa da su daga waje, sai dai kan abin da take samarwa, sarrafawa da kuma fitarwa zuwa ƙasashen duniya.

By ukarofi

Leave a Reply