Yadda rijiyoyin fetur 13 sun koma hannun gwamnati bayan sun gagara samun masu saye

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za ta mayar da rijiyoyin mai da iskar gas guda 13 cikin jerin rijiyoyin da ake bayar da lasisin haƙowa, bayan da suka gaza samun masu zuba jari a zagayen bayar da lasisin shekarar 2025.

An bayyana hakan ne ranar Talata a Abuja yayin taron buɗe tayin kasuwanci na zagayen bayar da lasisin haƙo mai na 2025, inda Babbar Jami’ar Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Mai ta ƙasa (NUPRC), Oritsemeyiwa Eyesan, ta ce daga cikin rijiyoyi 50 da gwamnati ta gabatar domin neman masu saka hannun jari, guda 37 ne kawai suka samu tayin.

Ta ce, “A ƙarshen wannan tsari, rijiyoyi 50 ne aka gabatar, amma tayin saka hannun jari ya shafi guda 37 ne kawai. Sauran rijiyoyi 13 za a mayar da su cikin jerin rijiyoyin da za a sake bayar da lasisi a nan gaba.”

Duk da cewa wasu rijiyoyin ba su samu masu neman lasisi ba, Eyesan ta bayyana cewa zagayen ya samu gagarumar karɓuwa, inda kamfanoni 143 suka shiga matakin ƙarshe na gabatar da tayin kasuwanci, bayan sun miƙa kusan tayi 200 kan rijiyoyin da aka bayar.

Ta bayyana cewa tun farko kusan kamfanoni 300 ne suka nuna sha’awar shiga tsarin, abin da ta ce ya nuna yadda masu zuba jari ke ƙara nuna amincewa da ɓangaren haƙo mai da iskar gas na Nijeriya.

A cewarta, bayan tantancewar farko, kamfanoni 196 ne suka cancanci shiga matakai na gaba, kafin daga bisani kamfanoni 143 suka kai ga gabatar da tayinsu na ƙarshe.

“Daga kusan kamfanoni 300 da suka nuna sha’awa, tantancewar farko ta rage adadin zuwa 196. Daga nan ne kamfanoni 143 suka shiga matakin tayin kasuwanci tare da gabatar da kusan tayi 200,” inji ta.

An ƙaddamar da zagayen bayar da lasisin haƙo mai na shekarar 2025 ne a watan Nuwamban 2025 bisa tanadin Dokar Masana’antar Fetur ta 2021 (PIA).

Rijiyoyin da aka bayar sun bazu a yankuna bakwai masu albarkatun mai na ƙasar, ciki har da rijiyoyi 16 a yankin Neja Delta, rijiyoyi 18 a yankunan ruwa marasa zurfi, guda ɗaya a zurfin teku, uku a yankin Benin Basin, huɗu a Anambra Basin, huɗu a Chad Basin da kuma huɗu a Benuwe Trough.

Tsarin karɓar tayin ya fara ne da buɗe shafin neman lasisi a watan Disamban 2025, sannan aka gudanar da taron masu ruwa da tsaki a Legas a watan Janairun 2026. An rufe rajista da tantancewar farko a watan Fabrairu, yayin da aka kammala tantancewar fasaha da kasuwanci a watan Maris. A ƙarƙashin tsarin bayar da lasisin, gwamnati na zaɓar waɗanda suka yi nasara ne ta hanyar duba girman kuɗin da suka yi alƙawarin biya, shirinsu na gudanar da ayyuka, ƙwarewar fasaha, ƙarfin kuɗi da kuma tabbacin aiwatar da ayyukan, domin tabbatar da cewa rijiyoyin sun shiga hannun masu zuba jarin da za su bunƙasa bincike da haƙo albarkatun mai da iskar gas a Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply