Duk da kammla kashi 98 na aikin bututun gas ɗin AKK babu ranar fara aiki – Rahoto

Spread the love

Daga MAHDI MSA MUHAMMAD

Shekaru shida bayan ƙaddamar da aikin bututun iskar gas na Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano (AKK), wanda aka yi wa kallon babban shirin da zai kawo ci gaban masana’antu da samar da makamashi, musamman a Arewacin Nijeriya, har yanzu ba a fara jigilar iskar gas ɗin ba, duk da iƙirarin da Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL) ke yi na cewa aikin ya kai kashi 98 cikin 100 na kammala aikin.

An ƙaddamar da aikin ne a shekarar 2020 da alƙawarin kammala shi cikin shekaru biyu, amma tun daga lokacin an sauya wa’adin kammalawa sau da dama sakamakon matsalolin tsaro, ƙarancin kuɗi, ƙalubalen fasaha da kuma yanayin ƙasa.

A cewar wani rahoto, duk da cewa an shimfiɗa bututun daga Ajaokuta da ke Jihar Kogi har zuwa Kano, har yanzu ba a kammala muhimman cibiyoyin da za su karɓi iskar gas da kuma kayan aikin da ke saman ƙasa da ake buƙata domin fara aiki ba.

Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na NNPCL, Andy Odeh, ya bayyana cewa an kammala shimfiɗa babban bututun iskar gas daga Ajaokuta zuwa Kano, kuma abin da ya rage shi ne kammala tashoshin da za su sarrafa iskar da kuma sauran kayayyakin da za su tabbatar da tsaron aikin.

Ya ce kamfanin na sa ran kammala waɗannan ayyuka nan gaba kaɗan, inda ya ƙara da cewa ana duba watan Satumba na wannan shekara a matsayin lokacin ƙaddamar da aikin, duk da cewa har yanzu babu tabbatacciyar ranar fara jigilar iskar gas.

A cewarsa, da zarar an kammala kayan aikin da ke saman ƙasa tare da gwajin bututun, za a fara jigilar iskar gas zuwa Gwagwalada a matakai, kafin daga bisani a faɗaɗa zuwa sauran yankuna.

Tushen aikin AKK ya samo asali ne daga Babban Tsarin Raya Iskar Gas na Nijeriya da gwamnatin tarayya ta amince da shi a shekarar 2008 domin bunƙasa amfani da iskar gas a cikin gida da kuma kasuwannin ƙetare.

Aikin, mai tsawon kilomita 614 da faɗin inci 40, ana kiyasta darajarsa ta kai dala biliyan 2.8, kuma shi ne mataki na farko na Babban Bututun Iskar Gas na ƙasa.

An tsara bututun ne ya taso daga Ajaokuta, ya ratsa Abuja da Kaduna kafin ya ƙare a Kano. An fara neman masu kwangilar aikin tun shekarar 2013, amma aikin ya fuskanci cece-kuce a shekarar 2017 bayan wata takarda da tsohon ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur, Dakta Ibe Kachikwu, ya aikawa marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ta fito fili, inda ya yi zargin cewa ba a bi ƙa’idoji yadda ya kamata wajen bayar da kwangilar.

Daga bisani, Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da kwangilar a watan Disamban 2017, kafin a sanya hannu a kan wasu sassan aikin a shekarar 2018.

Marigayi Darakta Janar na Kamfanin NNPC, Dakta Maikanti Baru, ya bayyana a lokacin cewa aikin zai zama ginshiƙin bunƙasa masana’antu da samar da makamashi a Gabas da Arewacin Nijeriya.

Tun bayan ƙaddamar da aikin, gwamnati da NNPC sun yi alƙawarin kammala shi a shekarar 2022. Daga baya aka ɗaga wa’adin zuwa 2023, sannan aka sake cewa zai kammala a ƙarshen 2024. Bayan haka aka mayar da ranar zuwa farkon shekarar 2025.

A watan Fabrairun 2026, Mataimakin Shugaban NNPCL mai kula da Harkokin Iskar Gas, Wutar Lantarki da Sabbin Makamashi, Olalekan Ogunleye, ya ce za a fara jigilar iskar gas cikin watan Yulin 2026, amma har yanzu hakan bai tabbata ba.

Bincike ya nuna cewa tashar AKK da ke Tamburawa a Kano ba ta wuce aikin katanga ba, duk da cewa ya kamata a ce ta fara aiki tun watanni da dama da suka gabata.

A wurin akwai hasumiyoyin tsaro, ɗakin janareta, ofisoshi da na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana, amma ba a fara manyan ayyukan gine-ginen tashar ba. An kuma ware wani fili kusa da tashar domin gina wata sabuwar cibiyar karɓar iskar gas.

A Jihar Kogi, inda aka fara shimfiɗa bututun, injiniyoyin aikin sun bayyana cewa sun fuskanci manyan ƙalubale kafin su kai ga kammala aikin.

Daga cikin matsalolin akwai garkuwa da ma’aikata domin neman kuɗin fansa, hare-haren ‘yan bindiga, tsaunuka, duwatsu, koguna da kwaruruka masu wahalar aiki.

Sun ce babban ƙalubale shi ne yadda aka ratsa Kogin Neja da bututun, wanda sai bayan amfani da fasahar Horizontal Directional Drilling (HDD) aka samu nasarar aiwatar da shi.

Masana harkokin makamashi sun bayyana cewa ci gaba da jinkirta aikin na iya jefa martabar Nijeriya cikin haɗari, musamman ganin cewa AKK na da muhimmanci wajen aiwatar da aikin Bututun Iskar Gas na Trans-Sahara, wanda ake sa ran zai bai wa Nijeriya damar fitar da iskar gas zuwa Turai.

Masanin tattalin arzikin makamashi, Bala Zakka, ya ce jinkirin ya hana Arewacin Nijeriya cin gajiyar dubban guraben aikin yi, samar da wutar lantarki da kuma bunƙasar masana’antu.

Ya ƙara da cewa, da an kammala aikin tun lokacin da aka tsara, Nijeriya za ta riga ta fara amfana da kasuwannin iskar gas na duniya, maimakon ci gaba da fuskantar ƙarin kuɗaɗen gudanar da aikin sakamakon hauhawar farashi da faɗuwar darajar naira.

Shi ma Farfesa Dayo Ayoade, ƙwararre a fannin dokokin makamashi na Jami’ar Legas, ya ce jinkirin aikin na iya shafar shirin gwamnatin tarayya na mayar da Nijeriya ƙasa mai amfani da iskar gas, tare da janyo matsaloli wajen biyan basussukan da aka karɓo domin gudanar da aikin.

By ukarofi

Leave a Reply