AI na ƙara haifar da sabbin barazanar cin hanci da rashawa – Shugaban EFCC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC), Ola Olukoyede, ya gargaɗi cewa duk da irin dimbin damar da Fasahar Basirar Wucin Gadi (Artificial Intelligence – AI) ke bayarwa wajen ƙarfafa yaƙi da cin hanci da rashawa, tana kuma ƙara haifar da sabbin barazana ta hanyar bai wa masu aikata damfara, laifukan kuɗi da safarar haramtattun kuɗaɗe damar amfani da ingantattun dabaru.

Olukoyede, wanda shi ne kuma Shugaban Cibiyar Hukumomin Yaƙi da Cin Hanci ta Yammacin Afirka (NACIWA), ya bayyana haka ne a yayin buɗe Taron Shugabannin Hukumomin Yaƙi da Cin Hanci na ƙasashen Yammacin Afirka na tsawon kwanaki biyu da aka gudanar a Hedikwatar ECOWAS da ke Abuja.

Ya ce saurin bunƙasar fasahar zamani da AI ya sauya yanayin cin hanci da rashawa, lamarin da ya sa ya zama wajibi hukumomin yaƙi da cin hanci a yankin su sabunta dabarun su domin tunkarar sabbin barazanar.

A cewarsa, ƙungiyoyin masu aikata laifuka na aiki ba tare da iyaka ba a ƙasashe daban-daban, yayin da kuɗaɗen haramtattu ke ratsa ƙasashe cikin daƙiƙu kaɗan, abin da ya sa tsoffin hanyoyin bincike da yaƙi da laifuka ba su ƙara wadatarwa.

“Fasahar AI ta sauya yadda ake samarwa, nazari da amfani da bayanai. Duk da cewa tana ba da dama wajen gano laifuka, tattara bayanan sirri, tantance haɗari da inganta ayyukan hukumomi, tana kuma haifar da tambayoyi kan shugabanci, ɗabi’a, gaskiya, amincin bayanai da shirye-shiryen hukumomi,” inji Olukoyede.

Ya ƙara da cewa sabbin fasahohi na bunƙasa tattalin arziki da kirkire-kirkire, amma kuma suna ba masu aikata laifukan kuɗi damar yin damfara, ɓoye bayanai da sauran laifuka cikin sauƙi.

Shugaban EFCC ya jaddada cewa dole ne hukumomin yaƙi da cin hanci su inganta ƙwarewa da fasahohin su domin su iya tunkarar dabarun ƙungiyoyin masu aikata manyan laifuka da ke amfani da fasahar dijital.

Ya kuma yi kira da a ƙara haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Yammacin Afirka, yana mai cewa cin hanci da rashawa ya zama matsala mai ketare iyakokin ƙasa, wanda ba za a iya magance shi yadda ya kamata ba sai ta hanyar haɗin kai.

Olukoyede ya bayyana cewa an shirya taron ne domin ƙarfafa shugabanci da haɗin gwiwar hukumomin yaƙi da cin hanci a faɗin yankin.

Ya ce taron ya nuna ƙudirin NACIWA na mayar da horas da shugabanni, musayar ilimi da gina ƙwarewar hukumomi a matsayin ginshiƙan yaƙi da cin hanci a Yammacin Afirka.

“Muna nuna cewa hukumomin yaƙi da cin hanci na Yammacin Afirka a shirye suke su ɗauki alhakin ƙarfafa tsarin gaskiya da riƙon amana a yankin,” inji shi.

Ya ce shugabanci mai nagarta a yaƙi da cin hanci bai tsaya ga bincike da gurfanar da masu laifi ba, har ma ya haɗa da gina hukumomi masu ɗorewa da za su iya jure sauye-sauyen siyasa da sabbin dabarun masu aikata laifuka.

Ya ƙara da cewa dole hukumomin su kasance masu bin doka, gaskiya da ƙwarewa yayin fuskantar rikitarwa da sababbin nau’ikan laifukan kuɗi.

A nasa jawabin, Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi (SAN), ya ce Yammacin Afirka na fuskantar wani muhimmin mataki inda jama’a ke neman ƙarin gaskiya, riƙon amana da ƙarfafa hukumomin gwamnati.

Ya bayyana cewa samun nasarar yaƙi da cin hanci na buƙatar shugabanci mai hangen nesa da ƙarfin hali, wanda zai tabbatar da ‘yancin hukumomi da kuma ƙara wa jama’a kwarin gwiwa.

Fagbemi ya gargaɗi cewa bai kamata a ɗauki mukamin gwamnati a matsayin hanyar tara dukiya ba, yana mai cewa dole jami’an gwamnati su kasance masu bayar da cikakken bayani kan yadda suke gudanar da dukiyar al’umma.

Taron ya haɗa shugabannin hukumomin yaƙi da cin hanci daga ƙasashen Yammacin Afirka, ciki har da wakilan ICPC, CCB da tawagogi daga Ghana, Saliyo, Senegal, Gambiya, Togo, Cape Verde da sauran ƙasashen ECOWAS.

Mahalarta taron na tattauna batutuwa da suka haɗa da fasahar AI, sauye-sauyen dijital, ‘yancin hukumomi, binciken sirri, cin hanci da rashawa na ƙetare iyakoki, haɗin gwiwar shari’a, dawo da kadarori da gyaran tsarin shugabanci.

Ana sa ran taron na farko na NACIWA zai ƙare da amincewa da Sanarwar Shugabanci ta Abuja, wadda za ta ƙunshi ƙa’idoji da matakan haɗin gwiwa domin ƙarfafa hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa a faɗin Yammacin Afirka.

By ukarofi

Leave a Reply