
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Zamfara ta aike da gaisuwar ta’aziyyarta ga al’ummar ƙauyen Sauna da ke Ƙaramar Hukumar Talatar Mafara, bayan wani mummunan harin ‘yan bindiga da ya yi sanadiyyar ajalin mutane 26 da raunata wasu guda huɗu.
Maitaimakin gwamnan jihar, Alhaji Mani Malam Mummuni Masamar Mudi ne ya kai gaisuwar a madadin gwamnatin jihar ga al’ummar ƙauyen a ranar Juma’a.
Da yake jawabi, Mummini Masamar ya jaddada aniyar gwamnatinsu ta ƙoƙarin kawo ƙarshen ayyukan ‘yan bindiga a faɗin jihar.
Ya ce, gwamnatin Zamfara ba ta taɓa yin wata tattaunawar sulhu da ‘yan bindiga ba, yana mai bayyana rashin gaskiya da cancanta a matsayin dalilan ɗaukar matakin nasu.
Haka kuma, ya yaba wa ‘yan ƙauyen bisa ƙwarin-gwiwa da kishin da ‘yan bijilante ɗinsu suka nuna wajen tunkarar maharan a musayar wuta da ta gudana a tsakaninsu, lamarin da ya tilasta wa ‘yan ta’addar janyewa daga farmakin nasu.
Akan haka ne mataimakin gwamnan ya bayar da tallafin Naira miliyan 1 ga ‘yan bijilanten domin taimaka wa ayyukansu.
Kazalika, ya tabbatar wa jama’ar cewa gwamnatin jihar za ta samar ababen tallafi domin iyalan waɗanda iftila’in ya shafa.
