Zargin sauya ɗan takarar ADC a Adamawa ya janyo zanga-zangar magoya bayan Omarana

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ana ci gaba da fuskantar sabon rikicin siyasa a Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Adamawa, bayan zargin cewa wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar na ƙoƙarin sauya ɗan takarar gwamna, Ambasada Injiniya Omar Suleiman, wanda aka fi sani da Omarana, gabanin zaɓen 2027.

A ranar Laraba, ɗaruruwan magoya bayan jam’iyyar sun gudanar da zanga-zangar lumana a birnin Yola, babban birnin jihar, domin nuna adawarsu ga abin da suka bayyana a matsayin yunƙurin maye gurbin ɗan takarar.

Masu zanga-zangar sun yi tattaki a manyan tituna da cibiyoyin gwamnati ɗauke da alluna masu ɗauke da saƙonni irin su “A’a ga sauya ɗan takara,” “A mutunta dimokuraɗiyyar jam’iyya,” da “Omarana ne ɗan takararmu.”

Sun jaddada cewa Omarana shi ne halastaccen ɗan takarar gwamnan ADC a Adamawa, tare da yin kira ga shugabannin jam’iyyar na ƙasa da su yi watsi da duk wani yunƙurin da suka ce na katsalandan daga wajen jam’iyyar, sannan su mutunta sakamakon zaɓen fidda gwani.

Da yake magana a madadin masu zanga-zangar, Shugaban ƙungiyar Frontier Movement Nationwide, Masu Umar, ya ce duk wani yunƙurin sauya ɗan takarar na iya jefa jam’iyyar cikin rikici kafin zaɓen gwamna na 2027.

Ya ce wajibi ne a mutunta sakamakon tsarin cikin gida na jam’iyyar, yana mai gargaɗin cewa za su yi amfani da hanyoyin da doka ta tanada domin kare haƙƙin ɗan takararsu.

Ita ma jagorar mata ta ADC a jihar, Damaris Yalawa, ta buƙaci shugabannin jam’iyyar su tabbatar da cewa an bar Omarana ya tsaya takara, tana mai cewa shi ne aka zaɓa ta hanyar sahihin tsarin jam’iyyar.

Yalawa ta kuma yi kira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) da ta tabbatar an bi ƙa’idojin zaɓe wajen amincewa da sunayen ‘yan takara, tana mai cewa ba za su amince da duk wani yunƙurin sauya ra’ayin mambobin jam’iyyar ba.

Hajiya Alisha Hamisu, wata magoyiyar jam’iyyar, ta bayyana cewa ADC na fuskantar wani mawuyacin lokaci da ke buƙatar a magance shi cikin hikima domin kare muradun jam’iyyar da kuma shirye-shiryen zaɓen 2027.

Ta ce idan ba a magance matsalar cikin gaggawa ba, hakan na iya shafar damar jam’iyyar a zaɓe, tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki su tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai sun ci gaba da wanzuwa.

Masu zanga-zangar sun kuma yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakin warware matsalar cikin gaggawa ba, za su ci gaba da bin hanyoyin da doka ta tanada domin kare abin da suka kira muradin mambobin ADC a Adamawa.

Sai dai wasu masu sa ido kan harkokin siyasa a jihar na ganin cewa rikicin na da alaƙa da saɓanin siyasa tsakanin tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, kan tasirin siyasa da shugabanci a cikin jam’iyyar a jihar Adamawa.

By ukarofi